Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

HIJABI LULLUBIN MUSULUNCI (1)


Mu'assasar Al-Balagh


Hakika Musulunci ya haifar da gagarumin sauyi a tarihin mace, wadda har ya zuwa yau ba a samu na biyunsa ba. Domin ta hanyar sa ne, ta samu damar dawo da mutunci da hakkokinta da aka raba ta da su a karkashin zaluncin zamanin jahiliyya na karnoni da dama. Ta haka ne Musulunci ya kwato mata hakkokinta ta yadda za ta yi rayuwa cikin mutunci karkashin tsarin rayuwa mafificiya.
A karo na farko a tarihi, mace ta samu damar amfana da hakkokinta na dan'Adamtaka a karkashin tsari da dokoki irin na Musulunci. An yaye wa mata kangin zalunci, kana kuma ta samu damar rayuwa a matsayin dan'Adam mai mutunci, daukaka kana mai matsayi kamar dai-dai da na namiji. To amma fa dole ne wannan 'yanci ya kasance cikin iyakokin Allah Madaukakin Sarki Wanda Ya ba wa mace dama, kana kuma Ya tsara mata hanyar da za ta iya ba da nata gudummawar wajen gina rayuwa, daukaka, tabbatar da gaskiya da kuma yada alheri.
To hakika wannan kuduri zai kasance ne kawai kamar wani mafarki da tatsuniya a wajen wadansu, idan har ba a karfafa shi da wasu ayoyi na Alkur'ani mai girma da hadisan Annabi da kuma Mutanen gidansa (Ahlulbait) tsira da amincin Allah su tabbata a gare su ) ba.
(1) A zamanin jahiliyya, al'umma tana ganin mace a matsayin wata bi-tsami, wani abu na la'ana, matatta-rin muggan ayyukan shaidan, ko kuma sukan kwatanta ta da matsayin wata dabba da aka halicce ta a yanayin dan'adam. To amma ko da Alkur'ani ya zo sai ya karyata wannan kuduri, wanda ya saba wa gaskiya da kuma hakika. Ya ci gaba da nuna cewa namiji da mace wasu irin 'yan tagwaye ne da suka fito daga mabubbuga da kuma manufa guda.
" Ya ku mutane ! ku bi Ubangijinku da takawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata....." ( Surar Nisa'i: 4:1)
" Shi ne Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya sanya daga gare ta, ma'aurata, domin ya natsu zuwa gare ta...." (Surar A'araf: 7:189)
"Kuma Allah Ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma Ya sanya muku daga matan aurenku diya da jikoki...."(Surar Nahali: 16:72)
Bayan bayyana matsayin mace a rayuwa da kuma samuwar dan'adam a fili, Alkur'ani mai girma ya yi kakkausar suka ga al'adar nan ta bisne 'ya'ya mata da rai, wato Wa'id[1]. "Kuma idan wadda aka turbude ta da rai aka tambaye ta, saboda wani laifi ne aka kashe ta?"(Surar Takawir: 81:8-9)
Kana kuma ya kawo karshen zamanin da ake kange mace daga aure har sai ta biya kudin fansar kanta ko kuma cikin zalunci a gaje ta bayan mutuwarta.
" Ya ku wadanda suka yi imani ! ba ya halalta a gare ku, ku gaji mata a kan tilas. Kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashen abin da kuka ba su...."(Surar Nisa'i: 4:19)
Sannan kuma ya yaye musu irin zalunci da wulakanta su da mazaje suke yi. Don haka ne ma Alkur'ani ya ba da muhimmanci mai girman gaske kan tausaya musu yayin mu'amala da su:
"....Kuma ku yi zamantakewa da su da alheri. Sa'an nan idan kun ki su, to, akwai tsammanin ku ki wani abu, alhali kuwa Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa."(Surar Nisa'i: 4:19)
Koda yake a da, talauci ma ya kan sa mutane su kashe 'ya'yayensu musamma ma 'ya'yaye mata, don haka Alkur'ani ya kawar da wannan al'amari ( daga kanta):
" Kuma kada ku kashe diyanku saboda talauci, Mu ne Mu ke arzurta ku da su..."(Surar An'ami: 6:151)
Kana kuma Musulunci ya bayyana cewa ma'aunin daukaka ba wai ya dogara kan mazantaka ba ne face kan imani (da Allah) da ayyuka na kwarai. Duk wanda ya aikata wani aiki to zai sami sakamakonsa, shi namiji ne ko mace:
" Lalle, Musulmi maza da Musulmi mata da Muminai maza da Muminai mata, da masu tawali'u maza da masu tawali'u mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu hakuri maza da masu hakuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu mata, da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonSa da yawa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma." (Surar Ahazabi: 33:35)
Kana Musulunci ya ci gaba da nuna cewa muminai sashensu majibincin sashe ne. Sun kasance masu yada alheri a tsakaninsu kana suna umurni da abu mai kyau, sannan suna hani da munana:
" Kuma Muminai maza da Muminai mata, sashensu majibincin sashe ne, suna umurni da alheri kuma suna hani daga abin da ba a so, kuma suna tsayar da salla kuma suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa. Wadannan Allah Zai yi musu rahama….." ( Surar Tauba : 9:71)
Hakika Musulunci ya tsaya wajen bayyana irin yanayin mu'amalar da ke tsakanin mace da namiji ta hanyar aure :
" Su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su…." (Surar Bakara: 2: 187)
" Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta mu ku matan aure daga kanku, domin ku nitsu zuwa gare su, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku..." (Surar Rumi : 30:21)
Baya ga tsara dokoki kan hakkokin da 'yancin mace, hakika Alkur'ani mai girma ya mai da hankali kan wajibcin girmamawa da kulawa gare ta, kana da kuma bata cikakkun hakkoki da 'yancinta.
Manzon Allah, Muhammad (s.a.w.a ) yana cewa :
"Babu wadanda za su girmama mata, face masu mutunci, kana babu wadanda za su cutar da su face marasa mutunci [2]"
"Kada ku nuna bambanci wajen kyauta a tsakanin 'ya'yayenku, hakika da za a ba ni zabi wajen taimako, lalle da na zabi mata ( don taimaka musu) [3] "
"Ba na tsammanin mutum zai samu karuwa a imaninsa, ba tare da kaunar mata sosai ba [4]"
Sannan bugu da kari, akwai tsarkakan nassosi masu yawan gaske da suke kira da a tabbatar da mace a kan matsayin da take da shi a cikin al'umma.
Kana kuma Musulunci ya ba da wasu muhimman abubuwa ga mace. Ya tsara mata sutura ta musamman don tabbatar da daukakarta da kuma kare mata mutuncinta daga lalacewa da rugujewa. Don haka ana iya cewa ta hanyar hijabi (Lullubin Musulunci), Musulunci ya sami cim ma manyan manufofi guda biyu: Na farko, ya kare mata akidarta, yayin da take aikata abubuwan da suka hau kanta na wajen ba da gudummawarta ga al'umma, ci gaba da kuma Sakon Musulunci da kuma gudanar da al'amurran da suka shafi rayuwarta gwargwadon yadda Musulunci ya tsara.
Na biyu, yana kare tsarkakan mace da kuma toshe duk wata hanya da za ta kai ga aikata duk wani aiki da zai kai ta ga fadawa ga munanan ayyuka; ko kuma ya juya ta ta zama wani makami da ke lalata al'ummar da take rayuwa a cikinta -kamar yadda yake faruwa a kasashen Turai -. Baya ga irin nasarar da hijabi ya samu wajen kare mace da kuma tsara mata irin suturar da za ta sa da kuma haramcin da Musulunci ya yi na cakuduwan (mata) da wadanda ba muharramansu ba, da dai sauran ka'idoji, za mu ga irin matukar kokarin da Musulunci ya yi wajen kare namiji da mace, da kuma dukkan al'umma, daga yaduwar munanan ayyuka da kuma rayuwar da ba ta da amfani.
Dangane da wadannan ka'idoji da dokoki, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
Dangane da wadannan ka'idoji da dokoki, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce da Muminai mata da su kawar da idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu ko ubanninsu, ko ubannin mazajensu, ko diyansu, ko diyan mazansu ko 'yan'uwansu, ko diyan 'yan-'uwansu mata ko matansu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai wadanda ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da kafafunsu, domin a san abin da suke boyewa daga kawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, Ya ku Muminai!, tsammaninku ku sami babbar rabo". (Surar Nuri: 24:30-31)
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, kana tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu (s.a.w.a) da Mutanen gidansa tsarkakku (a.s.).

MU'ASSASAR AL-BALAGH

B- Kalmomin Da Aka Yi Amfani Da Su A Wannan Bincike
1. Lullube mata a zamanin Jahiliyya: Wato kange mata daga musharaka cikin rayuwar al'umma da kuma hana ta 'yancinta.
2. Hijabin Musulunci: wato irin sanya tufafin da Musulunci ya yarda, wanda yake rufe dukkan jikin mace, amma ban da fuskanta da tafukanta.
3. Mahram: Muharrami yana nufin 'yan-'uwan mace da namiji wadanda aure ya haramta a tsakaninsu, kamar iyayen mutum, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, kawunnai,gwaggwannai, dan dan-'uwa ko 'yar'uwa, 'yar dan'uwa ko 'yar'uwa, kakan-ni, jikoki da sirikai.
4. Ajnabi ko Ajnabiyah (jam'insu shi ne ajanib ko ajnabiyat): Su ne wasun wadancan da aka ambata a sama wadanda aure ya halalta a tsakaninsu, misali 'ya'yan kawunnai ko gwaggwannai, ko kuma sauran dangi da bare. Ko kuma su ne wadanda babu wani haramci na Shari'a kan auratayya tsakaninsu.

1- Hijabin Musulunci: Yanayi Da Kuma Ma'anarsa

Hakika an cutar da mace ta manyan hanyoyi guda biyu, wadanda hakan su ne manya abubuwan da suka haifar da keta, wahala da zaluncin da suka faru gare ta cikin tarihi.
Abu na farko shi ne irin ganin da ake yi wa mace a matsayin wata wulakantacciyar halitta da maza kan mallaka don biyan bukatunsu na jima'i, kana a dai-dai wannan lokaci kuma ita ba wata aba ba ce face kawai wata na'ura ta haifuwar yara. Kana kuma ana kwatanta ta da cewa wata rumbu ce ta ajiye gudan jini. Kana wasu siffofin da ake fadi game da mace suna nan kamar haka: ana ganinta cewa shaidan ce cikin rigar dan'Adam, ko kuma hanya ta rashin biyayya a rayuwa….da sauransu. To amma babbar manufar duk wadannan abubuwa ba kome ba ne face kawai a wulakanta ta, bautar da ita da kuma kwace mata 'yanci da hakkokinta, kana da kuma kange ta daga musharaka cikin al'amurran yau da kullum.
Hakika, tarihin mace yana cike da surorin irin azabtarwa, wahalhalu da zaluncin da ya faru gare ta kamar yadda za mu yi cikakken bayani nan gaba.
Abu na biyu kuwa shi ne, ana ganin mace a matsayin wani abu ne kawai na jin dadin jima'i da kuma ribar duniya. Wannan mahanga kuwa ya samu asali ne daga irin al'adu da wayewa da ci gaban mai tonon rijiya na kasashen gabashin duniya (Turai). Domin idan har tsohon mahangan da ake wa mace na ganinta a matsayin wata wulakantacciya, kana mara wayewar halitta, wacce aka zalunta ta hanyar kwace mata 'yancinta, to ita kuwa sabuwar jahiliyyar wannan zamani sai ta yi mu'amala da ita ta hanyar da ya haifar da lalacewa da 'yancin zina ga mace. Hakika an yi amfani da hanyoyi daban-daban wadan-da suka hada da hanyoyin wayar da kai, makarantu, gidajen sinimomi, hanyoyi na dabara, dokoki, wasu tsare-tsare na siyasa na Turai da kasashen gabashin duniya don dasa wannan mahanga da kuma karfafa ta. An bi hanyoyi da matakai da dama wajen yada zinace-zinace, wanda hakan ba wai kawai ya tsaya ga zubar da mutunci da kimar mace ba ne, a'a, har ma da lalata al'umma da kuma zubar da kimar dan'adam a irin wadannan al'ummomi. Sannan daya daga cikin abubuwan da wannan al'amari yake haifarwa shi ne yaye mace da tura ta zuwa ga zinace-zinace ba tare da la'akari da kunya ko kuma wata doka ta Ubangiji ba.
Hakika wadannan irin zalunce-zalunce da wahal-halu da kuma zubar mata da kima da mutunci ya samu asali ne daga hanyoyi guda biyu: Hanyar Tsohuwar Jahilliya da kuma ta Sabuwar Jahiliyyar wannan zamani.
Lalle cikin tarihi, mace ba ta yi sa'a da kuma gamon katar da wani sako ko addini da ya kare mata mutuncinta, daidaitawa da kuma kiyaye matsayinta cikin al'umma ba, face addinin Musulunci, wannan sako na Allah Ta'ala, Ubangijin talikai. Don haka hijabi, kamar yadda wannan addini ya yi umurni da shi, ya kasance daya daga cikin hanyoyin tabbatar da irin wannan kulawan ta Ubangiji ga wannan madaukakiyar halitta kamar yadda za mu gani nan gaba.

2- Ka'idoji Biyu Kan Hijabi Mace.

Dangane da hijabi ga mace da kuma dangantakarsa da irin al'ummomin da suke kewaye da ita, hakika akwai manyan mahanga guda biyu kan kalmar hijabi cikin karnonin da suka gabata.

2- Mahangar Lokacin Jahiliyya Kan Hijabi.

Hakika kafin bayyanar Musulunci tsohuwar jahi-liyya ta samu daman kafa munanan manufofinta cikin tarihi, kana kuma mata sun dandani mummunan yanayi na zaluncin irin wancan lokacin. A wancan lokacin al'amari ya munana ta yadda aka kwace wa mace 'yancinta inda har ya kai ma ana ganinta kawai a matsayin wata haja ce ta saye da sayarwa, karkashin irin wannan mummunan tsari. An kwace mata kimarta na dan'Adamtaka, kana aka juya ta ta zamanto wata halitta kawai da mazaje suke amfani da ita don jin dadi, ko kuma a wani lokaci ma a matsayin baiwa.
Lalle koma dai mene ne za a fadi a matsayin shi ne abin da ya sanya mazaje suka shafe matsayin mata da kuma zaluntarsu a rayuwa a wancan lokaci da ya gabata, shin hakan ya faru ne saboda dalilai na tattalin arziki, sha'awa ko kuma dalili na ruhi ko addini, to al'amarin dai a fili yake, shi ne cewa shi wannan tozartarwa ga mace da kuma kwace mata hakkokinta, wannan kwace mata kimarta na dan'Adamtaka ya kai wani matsayi da mutumin wannan zamani ba zai iya suranta shi ba.
Zaluncin da ya faru ga mata yana yawo ne tsakanin wadannan al'amurori na haramci da wa'id da kuma abin da ke tattare da na mummunan akidu da dabi'u wadanda suke da yawa.
Zaluncin da ya faru ga mata yana yawo ne tsakanin wadannan al'amurori na haramci da wa'id da kuma abin da ke tattare da na mummunan akidu da dabi'u wadanda suke da yawa.
Wadansu kuma suna ganin mace a matsayin shaidan ne cikin tufafin dan'Adam, don kawai ta bauta wa namiji, kana ya samu biyan bukatunsa ta hanyarta, kamar yadda mutanen Jahiliyya suke gani.
Wasu kuwa suna daukan cewa jikinta na mutum ne, amma ranta na dabba ne. Wannan ra'ayi ya samo asali ne daga kasashen Turai kafin sauye-sauyen da aka samu.
To mai karatu, ya rage maka ka sauwara irin babban bala'in da ya faru ga mace, lokacin da ake ganinta a matsayin shaidan ko kuma wata dabba ko kuma wata haja abin sayarwa kamar sauran kayayyaki.
To wadannan su ne wadansu daga cikin irin wahal-halun da mace ta fuskanta karkashin irin wadannan munanan akidoji.
Lalle Alkur'ani mai girma ya ambaci wasu daga cikin wahalhalun da suka sami mace a karkashin al'ummar Jahiliyya ta Larabawa wanda kuma Musu-lunci ya yi kakkausar suka gare su:-
"Kuma idan aka yi wa dayansu bushara da mace, sai fuskarsa ta wuni baka kirin, alhali yana mai cike da bakin ciki. Yana boyewa daga mutane domin munin abin da aka yi masa bushara da shi. Shin zai rike shi a kan wulakanci, ko zai turbude shi a cikin turbaya? To, abin da suke hukumtawa ya munana".(Surar Nahali : 16:58-59)
"Kuma kada ku kashe 'ya'yayenku domin tsoron talauci. Mu ne ke arzurta su, su da ku. Lalle ne kashe su ya kasance kuskure babba". (Surar Isra'i : 17: 31)
"Kuma idan wanda aka turbude ta da rai aka tambaye ta : saboda wane laifi ne aka kashe ta". (Surar Takawiri : 81: 8-9)
Kana kuma an ruwaito Annabin rahama (s.a.w.a) yana cewa:
"Wata rana wani mutum mai suna Qais bin Asim al-Tamimi, ya zo wajen Manzon Allah (s) ya ce: " a lokacin Jahiliyya na kasance na bisne 'ya'yayena mata guda takwas.... [5]" .
Hakika za'a iya bayyana zamanin Jahiliyya na larabawa kafin zuwan Musulunci kamar haka :-
"An kasance ana bisne 'ya'yaye mata cikin mummunan yanayi; a kan bisne jariri da rai ! sukan yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen gudanar da wannan al'ada. Idan aka haifa wa daya daga cikinsu diya mace, to sukan bar ta har na tsawon shekaru shida. Daga nan sai mahai-finta ya yi umrnin da a yi mata ado a shafa mata turare da karyar cewa zai kaita wurin danginta ne ! To amma a dai-dai lokacin an riga an tona mata wani rami cikin rairayin sahara. A lokacin da suka isa sai mahaifin nata ya ce mata ta leka ramin, nan take sai ya tura ta cikinsa , kana ya rufe ta da kasa !
Wasu kuwa sukan yi amfani da wannan hanyar :- Wato lokacin da nakuda ta kama mace sai ta je ta zauna a bakin wani rami (da aka riga aka tona). Idan har ta ga abin da ta haifa mace ce, sai ta jefa ta cikin ramin, kana ta rufe ta da kasa. Idan kuwa namiji ne, sai ta dauke shi zuwa gida !
" Kana wadanda ba sa so su bisne 'ya'yayen nasu mata, sai su barsu cikin wulakanci har su kai shekarun da za su iya yin kiwo, to sai a sanya musu riguna masu gashi a tura su rairayin sahara don kiwon rakuma !
"Sannan wadanda ba sa so su tura ta kiwo, sai su yi amfani da wasu muggan hanyoyi don wulakanta ta. Misali idan yarinyar ta girma ta isa aure sai a yi mata aure, idan mijin nata ya mutu sai uban (waliyin) nata ya zo ya sanya mata wasu irin tufafi na musamman wadanda ke nuna cewa ba ta da wani 'yancin yin aure ba tare da yardar uban nata ba. Ta haka ne za a tilasta mata yin aure ba tare da sonta ba ! To idan shi uban nata ba ya son ya aure ta, to za ta zauna nan a daure har ta mutu, kana kuma sai ya gaje ta. Idan kuwa har tana son ta fanshi kanta daga irin wannan hali, dole ne sai ta bayar da wasu kudade don ta 'yantar da kanta.
" Wasu kuwa sukan 'yantar da matan, amma fa da sharadin ba za su taba yin aure ba sai dai da izinin waliyin nasu, ko kuma dole ne ta biya diyya. Wasu kuwa sukan ajiye bazawarai wadanda mazajensu suka mutu har sai wani daga cikin 'ya'yayensu kanana ya girma kafin su aurar masa da ita.
" Dangane da mace marainiya kuwa, sukan ajiye ta ne a wajensu kana su hana ta aure da burin cewa za su aure ta lokacin da matayensu suka mutu, ko kuma su sanya ta ta auri daya daga cikin 'ya'yayensu don saboda su sami dukiyarta.... [6]
Su kuwa Girkawa, suna ganin mace a matsayin wata doluwar halitta ce da bata da wani 'yanci guda-nar da duk wani al'amari.
Hatta wasu daga cikin falasafofin kasar Girka sun dauki kulle mace a cikin gida, kamar sanya ta cikin kurkuku ne. Wani mashahurin mai hikima na kasar Girka, Yosteen cewa yake:
" Muna auren mata ne kawai don su samar mana da halaltattun 'ya'yaye".
"Su kuwa Romawa, suna ganin matayensu a matsayin wani kaya maras kima da namiji ya mallaka. Sukan tafiyar da ita kamar yadda suke so. Sun taba yin wani taro a daya daga cikin majalisosinsu a birnin Roma don su tattauna kan al'amarin mata. Inda daga karshe suka kai ma natijar cewa ita (mace) kawai wata halitta ce da bata da kwakwalwa, kana kuma ba ta da wani rabo a rayuwar lahira. Ita kawai wata juji ce, ba za ta ci nama ba kana ba za ta yi dariya ba ko kuma bakin fadin wani abu ba. Dole ne ta tafiyar da rayuwarta cikin bauta da biyayya.
"Wasu daga cikin 'yan majalisar masanan Romawa sun fitar da wata doka da ta haramta wa mata mallakan fiye da rabin miskali na zinare. Dole ne ta sanya tufafi masu launi daban-daban kana kuma ba za ta yi tafiya a cikin keken dawaki na fiye da mil guda a wajen garin Roma ba sai dai in lokacin wani buki ne na gaba daya [7]"
Yayin da tarihin Turai yake magana kan kasar Girka ya nuna cewa a wani lokaci Bagirke guda ya kan ajiye mataye dari a gidansa.
Kana tsohon tarihin Iran ya bayyana faruwar wasu al'amurra makamantan wadannan na zamanin Jahilli-yar larabawa da kuma tsofin al'adun Turai. Idan ma dai akwai wani banbanci tsakaninsu to sai dai irin na bayani. A matsayin misali, yana da kyau mu yi dubi ga wadannan abubuwa:
"A zamanin da a Iran babu wani mutum da yake kange matayensa daga sauran mutane [8].
"Khosrow Parviz (wani sarkin gidan sasaniyawa) ya mallaki mataye kimanin 3000 a cikin fadansa, amma da haka ba su ishe shi ba. Domin duk lokacin da ya ke so ya kawata fadarsa, to sai ya rubuta wasika zuwa ga gwamnoninsa a inda zai ba su siffofin irin macen da yake so. A nan take za su kawo masa irin wannan mace da ya siffanta [9]"
A wasu shekaru da suka gabata a kasashen Turai, mutane suna da kuduri kamar haka:
Mace ba wai kawai wata alama ce ta rashin da'a, kana kuma matattarar muggan abubuwa da lalacewa ba ne kawai, face ma dai ita ce asalin duk wani bala'i da ka iya samun dan'Adam. Ita ce ummul aba'isin din duk wani tashin hankali da wahala ga mutanen da suke bayan kasa. Sannan wani daga cikin Paparomo-min farko mai suna Tirroliyan ya yi cikakken bayani kan matsayin Kiristanci dangane da mata. Ya ba da gurbataccen ra'ayin Kiristanci dangane da mace; ita ce hanyar da Shaidan yakan bi wajen shiga ruhin mutum. Ita ce wacce ta ingiza mutum zuwa ga haramtacciyar bishiyar nan (da aka hana Annabi Adamu (a.s) cinta), aka saba wa umurnin Allah, wannan ita ce mace [10]".
Dangane da matsayin mace a shekarun da suka wuce ne, malamin falsafan nan na Biritaniya Herbert Spinser yake fadi a cikin littafinsa na "Describing Sociology" cewa:
Hakika a karni na sha daya a Birtaniya, a kan sayar da mace (ga wanda zai aure ta) kana kuma a dai-dai wannan lokacin kuma sai kotuna, wanda dama su ke karkashin majami'ai ne, suka kafa wata doka wacce ta ba wa shi mijin daman chanzata ko kuma ba da hayar matar tasa ga wani namiji daban na wani kayyadad-den lokaci" [11].
Lalle kan wannan mummunar dabi'a ga mace wanda ya hada da tsoratarwa, kulle ta a cikin gida da kuma kange ta daga duk wani nau'i na rayuwa da jin dadi, domin kuwa tarihi ya hakaito kange mace da aka yi, wato kange ta daga taka rawa cikin al'amurran rayuwa, da kuma hana ta 'yancin da take da shi.
Hakika irin wannan bakar akida ta kange mace da ya faru a zamanin jahiliyya, da kuma duk fadin duniya har da kasar Iran (ta wancan lokacin), Indiya, Masar, Turai da kuma kasashen larabawa kana da kuma irin yadda ake tafiyar da mace, shi ya ba da dama wajen kirkiro kungiyoyin kira ga kwato wa mata hakkinsu. To amma irin lamurran hijabi da kuma kula da mace da Musulunci ya zo da shi, ya saba wa irin kangewar lokacin harem, wa'id da kuma lokacin cinikin bayi inda mata suka wahala da gasken gaske.

Mahangar Musulunci Dangane Da Hijabi

Hakika, irin nau'in hijabi (kangewa) da Musulunci ya dauka, nesa ba kusa ba, ya saba wa irin nau'in kangewar zamanin Jahiliyya da kuma mummunan irin yanayin da ya wanzu a fadojin wasu sarakunan Umayyawa da Abbasiyawa dangane da amfani da mata don cim ma burinsu na sha'awa. Kai hatta ma dai hakikanin wannan kalma ta hijabi, ba ta shiga rayuwar Musulmi ba face kwanannan. To koma dai mene ne za a ce dangane da mace, al'amarin dai guda ne cewa saboda irin muhimmancin da Musulunci ya bawa mace, shi ya sa har ya tsara mata wani irin nau'in tufafi, wanda haka yana nuna irin girma da daukakan da Musulunci yake ganin mace tana da shi, da kuma kula da tsabtarta.
Lalle dai a Musulunci, da kuma duk abin da ya kunsa, babu wata doka ko ka'ida da ta hana mace musharaka cikin al'amurran rayuwa, ko kuma ya tsare ta a cikin gida kamar yadda ya faru a zamanin Jahiliyya. Hatta ma dai wannan kalma ta hijabi kwanan nan aka fara amfani da ita cikin akidar Musulunci [12].
Bugu da kari kan irin tufafi na musamman da mace take sa wa yayin da za ta fita daga gidanta- kamar yadda za mu yi bayani nan gaba- to Musulunci ya yi amfani da kalmar "sitr" (lullubi) ne ga wannan irin aiki.
Hakika Musulunci ya wajabta wa maza da mata da su kawar da idanuwansu daga kallon juna, face dai matayensu, mazajensu ko kuma muharramansu. A bangare guda kuma, Musulunci ya wajabta wa mace sanya hijabi, kana a daya bangaren kuma ya sanya wasu dokoki ga shi ma namijin.
Idan har an tsara wa mace wani nau'i na tufafi don ta kare kyawun jikinta; to shi kuma namiji a daya bangaren, an wajabta masa kawar da idanunsa daga kallon mataye, face dai muharramansa da kuma kare farjinsa.
Don samun daidaituwar wannan kalma ta hijabi da ainihin manufan Musulunci da kuma abin da yake nufi, to yana da kyau mu yi bayanin cewa: Lullubi da kamewa a Musulunci ya hada da maza da mata ne; to amma yanayinsu ya sha banban ne ta yadda dai za su iya kiyaye kyawawan dabi'u, kare dabi'u da kuma girmama matsayin mace a dukkan rayuwa. Domin shi Musulunci ba ruwansa da tsarewa ko kuma kange mace daga tafiyar da 'yancin da Allah Ya bata, kana a cikin tsari da ka'idojinSa, babu cutarwa da kaskantar da darajar mace. Hakika ya zamanto abin alfahari ga Musulunci, cewa saboda tabbatar dokokinsa ne aka kawo karshen yanayin wulakanci da bautar da mata, da mazaje suke yi a zamanin Jahiliyya, wanda ya bakanta tarihin dan'Adam, kafin bayyanar Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma sakonsa.
A takaice za a iya fassara hijabi (lullubin) Musulunci da cewa wani irin nau'i ne na sutura da kuma takaita alaka tsakanin maza da mata, wadanda ba muharraman juna ba, da sanya mace a tsarkakakken tafarki na girmamawa da kuma tabbatar mata da 'yancinta.


1. "Wa'id" a larabce yana nufin bisne 'ya mace da rai. A zamanin jahiliyya, Larabawa sun kasance suna aikata wannan dabi'a ta hanyoyi daban-daban. To lokacin da Musulunci ya zo sai ya hana su aikata wannan mummunan dabi'a.
2. Saeed Afghani cikin littafin " Islam wal Mar'ah (Musulunci da kuma Mace) ya ruwaito shi daga Tirmizi.
3. Kamar na sama, Jami al-Saghir.
4. Shaikh Saduk cikin litafinsa "Man la Yahdhuruhu al-Fakih, juzu'i na 3 , babi na 103 Hub al-Nisa (Son mata).
5. Shahid Sayyid Kutb cikin littafin "Fi Dhilal al-kur'an", juzu'I na 8, shafi na 479, bugun Darul Ihya al-Turath al-Arabi, 1971, Beirut.
6. "Al-Mar'a fi jami al-Adyan wal Usur" na Muhammad Abdulla Maqsud, shafi na 38, ya ciro shi daga littafin "Woman During History", shafi na 41.
7. Kamar na sama, ya ciro daga littafin "The Right of a Husband Upon His Wife and the Right of a Wife Upon Her Husband" (Hakkin miji akan matarsa kana da kuma hakkin mata akan mijinta) na Taha Abdullah Afifi, shafi na 12-13.
8. "Nizamul Hukuk al-Mar'a fil Islam" na Shahid Sheik Murtadha Mutahari, shafi na 269, bayan bugun farko, 1404 B.H, Tehran. 3- "Mas'alat al-Hijab" na Shahid Mutahari, shafi na 49, bugun farko 1407, B.H, Tehran.
9. Kamar na sama, shafi na 87, ya ciro daga littafin "Iran During Sassanian Period".
10. Mujallar al-Ifaf, adadi na 9, shafin na 25.
11. "Al-Mar'a fi jami'i al-Adyan wal usur" na Muhammad Abdullah Maksud, shafi na 48.
12. "Mas'alat al-Hijab", na Shahid Mutahari.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
7+8 =