Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

MATASA DA RAYUWA


Mu'assasar Al-Balagh


Dubi Cikin Abubuwan Da Suke Kewaye Da Matasa

Tun lokacin da na bude idanuwana a kan abubuwan da suke kewaye da ni na rayuwa, kana tun lokacin da na fara fahimta da kuma gano motsin abubuwan da suke kewaye da ni, tun daga lokacin na fara hada tunani da kuma gano dukkan abubuwan da na sadu da su...
Wannan duniya mai girma da daukaka da ta kunshi: sama da taurari, rana da wata, ruwa da iska, haske da duhu, kasa da tsirrai, koguna da ruwan sama, bishiya da nau'o'in dabbbobi daban-daban, mutane da suke raye a al'ummance, suna magana kana kuma suna fahimtar da junansu, sannan kuma suna saye da sayarwa tsakaninsu...
Wadannan abubuwa da suka saba da junansu... da suke cike da kyau da tsari, su suka sanya ni cikin tsananin tunani...kai suka sanya ni ina tambayan kaina: shin me ya sa ne ba zan fadada tunanina a kansu ba da kuma yin tunani kan girma da kuma daukakan wadannan halittu masu ban mamaki da suke kewaye da ni ba...kai me ya sa ne nake musu kallon daidaiku...ashe su ba abubuwa ne da suke tabbatar da cikan junansu ba...ashe su ba abubuwa ne da suke koyar da ni abubuwa da yawa ba...a takaice dai, me ya sa nake kallonsu a matsayin abubuwan da ba su da alaka da junansu?
Lalle gaskiya ce, cewa cikin dukkan abin da na sadu da shi akwai abubuwan al'ajabi da sanya tunani a cikinsa... hasken rana...zubowar ruwan sama... fitowar tsirrai da kuma girmansu...nau'o'in furrai da kuma kamshinsu...launin sama...ja-ja-ja-jan fitar rana...duk wadannan suna da ban mamaki.
Me ya sa aka samu wadannan halittu da kuma irin wannan bambance-bambance...shin wannan wani irin kyau ne na koli?
Kash! Ya ya girman wannan irin yanayi zai kasance, idan da a ce na fahimce su tun lokacin da aka haife ni ko kuma lokacin da na fara ganinsu?
Hakika na zo ne daga wata duniya ta daban...daga duniyar mahaifa... daga duniya ma'abuciyar duhu da take kange daga wannan duniya...
A halin yanzu ina jin wajibcin fahimtar wancar duniya...duniyar mahaifa wacce ban kasance ina tunaninta ba, kuma in fahimci wani abu daga cikinta ba. Lalle ina rayuwa cikinta ne ba tare da masaniya, ko nufi ko dogaro da kai ba...na kasance dan tayi ne da ke rayuwa a kan jinin mahaifiyarsa... tana rainonsa da kyau. Wannan ma wata rayuwa ce da ban san kome daga cikinta ba, face dai a halin yanzu na fahimci falalar wannan kulawa ta Ubangiji, da kuma kokarin mahaifiyata da ta rike ni cikin mahaifarta har na tsawon watannin tara, tana ciyar da ni da jininta, kana kuma tana mai kokarin ta ga na wuce wannan mataki cikin koshin lafiya...
Hakika na kasance ba ni da wani iko a wancar duniya da ban san kome ba dangane da ita ba...ba ni da karfi cikin samar da wani abu ko kuma zabi cikin yadda yanayina zai kasance, kuma ba ni da ikon samar wa kaina abinci ko isa ga iska ko kuma kare kaina daga hatsari. Don kuwa na kasance dan tayi ne, kamar kwai cikin injin kyankyasa ko kuma kamar hatsi a cikin kasa...na tashi ne bisa kulawa ta Ubangiji, sannan kuma mahaifiyata tana hakura da ni kan abubuwan da na ke mata alhali tana mai farin ciki, tana mai zagaye ni da so da kauna da kuma jira, tana mai kirga kwanaki don ta sadu da ni...
Hakika na kasance a wancar duniya mai cike da duhu kana kuma ban san kome a kanta ba, karkashin kulawa da kauna iri biyu: kauna ta mahaifiyata da kuma kauna ta Ubangiji...
Na fara rayuwa ne karkashin inuwar so da rahama...lalle a halin yanzu ina jin girman wannan soyayya da kuma falalar wancan rahama da kuma kula. Ina jin lalle ina da bashin wanda ya nuna min wannan soyayya da kuma kulawa, kana kuma ya min guzuri da jininsa duk tsawon zama na cikin wannan yanayi ba tare da na san inda na ke ba, ko kuma tunanin wani abu daga cikin al'amurran rayuwa ta ba...
Lalle wannan babban kyautatawa ce mai girma, lalle ya zama wajibi in ce: "shin, kyautatawa na da wani sakamako, face kyautatawa"...kai lalle ya zama wajibi in ce: inkarin wannan kyautatawa sabo ne da kuma kauce wa hanya wanda ya cancanci azaba.
Lalle wajibi ne in kasance mai godiya...kana kuma in so wanda ya nuna min irin wannan so da kuma kyautatawa...

Dalilan Girman Ubangiji da kuma Tsari:

Daga wancan duniya (duniyar mahaifa) zuwa duniyar rana, haske, hankali, nufi da dogaro da kai... lalle malamai sun bude mana kofofin sanin wannan duniya ta hanyar irin bincike-binciken da suka yi ta gudanarwa, sannan kuma suka bayyanar mana da sirruka da kuma abubuwan da suka shige mana duhu na dabi'a da kuma abubuwa masu rai; irinsu dabbobi da tsirrai. Kamar yadda kuma suka bude mana kofar sanin duniyar 'yan'Adam da abubuwan mamaki na cikinta da kuma karfin fahimta, magana da kuma tunani...
Hakika karanta irin wadannan abubuwa da malamai suka binciko mana, zai sanya mu cikin tsananin mamaki, kuma za su fitar mana da girman Ubangiji Mahalicci da kuma samuwar Wanda Ya tsara wannan duniya...
Daya daga cikin wadannan malamai mai suna Karisi Maurisun ya wallafa wani littafi da ya ba shi sunan "al-Ilmu yad'u lil-Iman". A cikin wannan littafi, malamin ya yi bayani kan girman tsarin Ubangiji ga wannan duniya, inda ya tabbatar mana cewa dukkan wani abu da yake wannan duniya yana nuni ga girman Mahaliccinsa ne...lalle mutum yakan fahimci samuwar Allah da kuma girmanSa yayin da yake karanta wannan littafi...
Wannan marubuci yana cewa:
"Duniya takan juya sau guda a duk sa'o'i ashirin da hudu, ko kuma abin da ya yi daidai da mil dubu a ko wani awa guda. To amma a halin yanzu an kiyasta cewa tana juyawa da abin da ya yi daidai da mil dari kawai a duk sa'a guda. To amma me ya sa ba hakan ba? Don haka, a irin wancan hali, dare da ranarmu za su kasance masu tsawo fiye da yadda suke a halin yanzu har sau goma. A irin wannan hali, rana za ta kona tsirranmu a ko wace rana, sannan da daddare kuwa, dukkan tsirrai za su daskare...
Hakika rana wacce ita ce mabubbugan dukkan rayuwa, za ta kai darajar zafi da ya kai kimanin 12,000 ma'aunin faranhait, kuma kasa tana da nisa daga gare ta ta yadda za mu iya samun zafinta kamar yadda ya kamata. Wannan nisa tabbatacce ne kuma mai ban mamaki, sannan wannan canje-canje ya kan afku ne cikin miliyoyin shekaru; ta yadda rayuwa za ta ci gaba kamar yadda muka fadi. Idan darajar zafi ya karu a kasa da kimanin daraja hamsin a shekara guda, to dukkan tsirrai za su mutu tare da 'yan'Adam don zafi ko daskarewa.
Sannan kuma kasa takan kewaya rana kimanin mil goma sha takwas a ko wace dakika guda. Da a ce adadin kewayar tata zai kai misalin mil shida ko kuma mil arba'in a ko wace dakika, to da nisanmu da rana ko kusancinmu da ita zai kasance ta yadda zai hana wanzuwar irin wannan rayuwa ta mu da ita".
Sannan kuma wannan babban malami ya ci gaba da ce wa: "Nisan wata daga gare mu ya kai kimanin mil 240,000...da a ce nisan wata daga gare mu mil 50,000 misali, maimakon wannan nisa da a halin yanzu yake tsakaninmu da shi, to da tsawonsa ya kai karfin da ambaliyar ruwa za ta mamaye dukkan kasar da take karkashin makwararan ruwa ta sau biyu a rana, har ya girgiza duwatsu...kuma da duniya ma ta ruguje saboda wannan bala'in...".
Lalle yana da kyau ko wane daya daga cikinmu ya yi tunani yayin da yake karanta wannan hakika na ilimi, ya tambayi kansa ya ya aka yi aka sami irin wannan tsarin...kuma Wane ne Ya sana'anta hakan?
Hakika Alkur'ani mai girma ya amsa mana wannan tambaya, yayin da yake ce wa:
"...bisa sana'ar Allah Wanda Ya kyautata kowane abu...". (Surar Namli, 27: 88)
"Shi ne Wanda Ya halitta sammai bakwai, dabakoki a kan juna, ba za ka ga goggociya ba a cikin halittar Allah Mai rahama..." (Surar Mulk, 67: 3)
"Kuma rana tana gudana zuwa ga wani matab-baci nata. Wanda kaddarawar Mabuwayi ne, Masani. Kuma da wata, Mun kaddara masa man-ziloli, har ya koma kamar tsumajiyar murlin dabino, wadda ta tsufa. Rana ba ya kamata a gare ta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukkansu a cikin sarari guda suke yin iyo". (Surar Yasin, 36: 38-40)
To idan wannan ita ce duniyar kasa da sama, bari mu koma ga kogi da kuma abubuwan da suka kewaye mu.
Lalle wani irin kyau ne wannan duniya take da shi, duniyar da take cike da dabbobi, kifaye, lu'u-lu'u da murjani...
Hakika bincike da karatuttukan da kwararrun malami suka gudanar sun kai su ga gano abubuwan ban mamaki na wannan duniya...abubuwan da suke sanya mutum cikin tunani da mamakin girman wadannan sirrori da suke tattare da wadannan halittu na cikin ruwa.
Wannan sanannen malami (Karisi Maurisun) cikin wannan littafi nasa mai suna "al-Ilmu Yad'uw lil-Iman" ya nakalto mana wani labari dangane da kifin salmon da kuma macijin ruwa, inda yake bayyana cewa:
"Bayan binciken da suka yi kan wadannan kifaye, malamai sun gano abubuwa masu ban al'ajabi kwarai. Wadannan kifaye su kan haihu a cikin kogi, amma sai su tafi su rayu na shekaru cikin teku, sannan daga baya su dawo cikin kogin da aka haife su. Kuma idan aka dauko su daga wannan kogi zuwa wani kogi na daban wanda suke hade, za su dinga iyo har sai sun koma cikin kogin da aka haife su.
Lalle sun san inda aka haife su, kuma suna da alaka da wajen, don haka suke neman wurin har sai sun koma wajen; don su rayu cikinsa".
Wannan malami ya sake kawo wata kissa mai ban mamaki dangane da rayuwar macijin ruwa...
Macijin ruwa ya kan yi hijira daga kogin da aka haife shi bayan ya girma, zuwa wani guri mai nisan gaske, inda zai je can ya rayu har ya mutu. Bayan isansu wannan guri da kuma haihuwa a wajen, 'ya'yayensu sukan sake shafe wannan tafiya mai nisan gaske su dawo inda aka haifi iyayensu, don su rayu a wajen. Ta haka ne dai wadannan halittu suke rayuwa.
Babu shakka wannan kissa ce mai ban mamaki wacce za ta bar mu cikin tsananin tunani da kuma tambayoyin da Alkur'ani mai girma ya amsa su cikin wadannan ayoyi:
"...Ubangijinmu Shi ne Wanda Ya bai wa dukkan kome halittarsa, sa'an nan Ya shiryar". (Surar Daha, 20: 50)
Lalle Allah Shi ne Wanda Ya shiryar da shi da kuma ba shi irin wannan ilimi.
Hakika wadannan lamurra suna bayyana mana ma'anar fadinSa Madaukakin Sarki cewa:
"...Malamai ne kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa...". (Surar Fadir, 35: 28)
Hakika ba za mu taba sanin Allah Madaukakin Sarki ba sai ta ilimin nan dai da Alkur'ani mai girma ya kiraye mu da mu neme shi, kamar kuma yadda ya kiraye mu zuwa ga tunani da kuma amfani da hankali wajen sanin Allah Madaukaki, sanin halittunSa da kuma fahimtar littafinSa mai girma:
"Shin to, ba za su kula da Alkur'ani ba, ko kuwa a kan zukatansu akwai makullansu?" (Surar Muhammad, 47: 24)
Hakika babban abin da zai kasance mana shamaki tsakaninmu da Ubangiji Tabaraka wa Ta'ala da kuma fahimtar littafinSa, shi ne jahilci, don kuwa daga lokacin da muka samu rabonmu na ilimi, kofofin sanin Allah za su budu mana, kana kuma hasken littafinSa zai haskaka zukatanmu.

Dubi Cikin Zatin

Dole ne in fahimtar da kaina, in san mutumci da kuma matsayina a rayuwa...lalle ni mutum ne, kuma babu shakka mutum yana da matsayi mai girman gaske cikin rayuwa, don haka yana da babban nauyi a rayuwarsa. Hakika an haife ni cikin mutumci da daukaka... lalle Allah Madaukakin Sarki ya arzurta ni da dukkan wadannan hakkoki, kamar yadda kuma Ya arzurta ni da wani yanki na wannan rayuwa ta duniya. Allah Ta'ala Yana ce wa:
"Kuma lalle ne Mun girmama 'yan'Adam, kuma Muka dauke su a cikin kasa da teku, kuma Muka arzurta su daga abubuwa masu dadi, kuma Muka fifita su a kan masu yawa daga wadanda Muka halitta, fifitawa". (Surar Isra', 17: 70)
Sannan kuma kamar yadda aka halicce ni a kan fidira (hanya madaidaiciya), ina tsarkakakke daga dukkan sharri da mugun nufi, haka kuma aka halicci sha'auce-sha'auce da ji-a-jika tare da ni. Kana kuma na ci gaba da girma kana kuma kwakwalwata ta ci gaba da buduwa. Da wadannan ne na ci gaba da rayuwa...lalle hakki na ne in yi cikakken bayani dangane da dukkan wadannan abubuwa...sannan kuma in fahimci cewa ina da babban nauyin kulawa da kuma kiyaye wannan farar takarda ta rayuwata...
Lalle mutumci da kuma rayuwata ta gobe amana ce da take hannuna, ina da 'yancin tafiyar da ita kamar yadda nake so, sannan kuma in ja-goranci kaina duk yadda na so. Hakika hanyoyin rayuwa suna da yawa, akwai hanyoyin bata da kauce wa hanya, kana kuma akwai na alheri da shiriya.
Da dama daga cikin mutane sun kauce wa hanya, alhali kuwa tun ba su girma ba, wasunsu ma ba su wuce shekaru goma sha bakwai na rayuwarsu ba. Sun kasance masu zuwa kulob-kulob da kuma biyan sha'awarsu ta hanyoyin da ba su dace ba...
Lalle jahilci ko ji-ji da kai sun mamaye wadannan mutane, ko kuma sun bar borin mafarki da wahami ya hau kansu, ko kuma sun bari jin dadi da sha'awa sun ja-gorance su zuwa wuta, da kuma bata takardun ayyukansu. Hakika cibiyoyin binciken laifuffuka sun tabbatar da irin wadannan yanayi, ta yadda har al'umma suke kallon masu irin wadannan halaye kallo na wulakanci da cin mutumci. Da wuya ka ga wanda yake musu kallo tausayawa da kuma kokarin tsamo su daga irin wannan hali da suke ciki.

Ya ya Zan Yi Mu'amala Da Sha'awa Da kuma Karfina?

Zatin dan'Adam yana dauke da shu'urin so da kuma ki, yarda da kuma fushi, sha'awar abinci da kuma jinsi, son kai da iko, son dukiya, da kuma son doruwa a kan sauran mutane. Babu shakka irin wadannan abubuwa su ne suke tura mutum zuwa ga sharri da kuma munanan ayyuka; kamar yadda kuma suke tura shi zuwa ga ayyukan alheri da kuma abubuwan da shari'a ta yarda da su.
Don haka matsayi mafi inganci shi ne mu dinga tunanin karshen al'amari kafin mu je ga aikata shi, don mu san mene ne sakamakon wannan abin da muke son aikatawa, shin sharri ne ko alheri...
Kamar yadda kuma yana da kyau mu dinga amfani da kwarewar da wasu suka samu kan wannan abu da kuma shawartar wadanda muka yarda da su; kamar uba, uwa, dan'uwa, abokai, malamanmu, kwararru kan lamarin da dai sauransu.
Akwai abubuwa da dama da suke motsa dan'-Adam zuwa ga fushi, kiyayya, son kai, aikata laifi da kuma sanya kai cikin ayyukan da ba zai iya tsira daga mummunan sakamakonsu ba.
Tana iya yiwuwa wahami da kuma rashin tabbaci su auri mutum, ta yadda zai dinga kitsa wasu abubuwa da ba za su iya tabbatuwa ba ko kuma burace-burace don cimma biyan bukatan sha'awarsa, da suka hada da son dukiya, ko kuma shahara ko kuma wani matsayi da dai makamantan hakan. Don haka sai ya bata lokaci da dukiyarsa ba tare da ya samu wannan abu da yake burin samu ba, face ma dai dukkan wadannan abubuwa su tafi a banza.
Kana kuma tana yiwuwa sha'awa da kuma burace-buracensa na son jin dadi su sanya shi sabawa da wasu munanan dabi'u, kamar shan muggan kwayoyi, taba, zinace-zinace da sauran ayyukan da za su sanya shi cikin nadama da bala'i, ta yadda ba zai taba fahimtar haka ba sai bayan da lokaci ya kure.
Hakika yana daga cikin hikima da kuma sanin ya kamata kar mutum ya sake aikata kuskuren da ya riga ya aikata kuma ya ga sakamakonsa, kamar yadda kuma ya kasance yana daga cikin hikima kada mutum ya aikata kuskuren da waninsa ya aikata...lalle kwarewar makaranta tana koyar da mutum isa ga manufa da kuma yin kuskure. Don haka ya hau kansa ya yi amfani da kuskurensa da kuma kuskuren sauran mutane don gyara kansa da kuma tsira daga fadawa cikin kuskure.
Masu iya magana suna cewa: "Wanda ya jarraba abubuwan jarrabawa, to ya tsira daga nadama".
Imam Ali (a.s.) yana ce wa:
"Mai samun rabo shi ne wanda ya wa'aztu da waninsa" [1] .

Girmama Halin Mutum:

Hakika mafi girman da kuma daukakan abin da mutum zai iya mallaka a rayuwarsa shi ne hali da kuma mutumcin kansa, hakan kuwa wata amana ce
da take a kan wuyansa wacce Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka shi da ita. Sannan kuma Ya haramta masa ha'intar kansa ko kuma kaskantar da ita da kuma ha'intar abin da Ya ba shi na kwarewa.
Imam Sadik (a.s.) ya yi bayanin wannan al'amari mai muhimmanci cikin fadinsa ce wa:
"Allah Madaukakin Sarki Ya bar (halalta) wa mumini dukkan kome in ban da wulakantar da kansa [2]".
Lalle babban nauyin da ke kan mutum dangane da kan kansa shi ne ya kiyaye abin da zai zubar masa da mutumcinsa cikin al'ummar da yake raye a ciki. Don kuwa ayyukansa suna nan a kan idanuwan al'umman da yake tare da su, kada ya aikata wani abin da zai zubar masa da mutumcinsa ta yadda shi ma da kansa zai yi dan da-na-sanin wannan aiki.
Kamar yadda hanyoyin girmama zatin dan'Adam da kuma samar da daukaka ga mutumcinsa suke da yawa, haka ma hanyoyin ha'intar kai da kuma zubar da mutumci suke da yawa...
Misali, karya da ta'addanci a kan al'umma, ya kan haifar da wulakantar da kai, haka ma aikata muggan ayyukan da suka saba wa dabi'u na kwarai, yarda da wulakanci ko don saboda neman kudi, jin dadi ko matsayi, duk hakan suna haifar da wulakanci, munafunci, tsoro...da dai sauransu.
Haka nan kuma jin kaskanci da kuma sanya wa zuciya tunanin gajiyawa ta rashin iya aikata wani aiki, hada kai cikin aikin alheri da kuma hidima ga al'umma, duk hakan sukan kashe zuciyar mai yin su.
Don kuwa Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta dukkan 'yan'Adam da karfi da kuma iyawa, don haka ya rage musu ne kawai su yi amfani da su wajen cimma manufarsu ta rayuwa. Don haka ba ya halalta gare su da su yi wasa da karfi da ikon da Allah Ya ba su...
Hakika Allah Madaukakin Sarki ba Ya haramta wa bayinSa ni'imominsa...wasu suna da karfin fahimtar ilimin magani, wasu kuwa ilimin yare, wasu kuma karfin kirkiro abubuwa suke da shi. Sannan wasu kuma karfin kasuwanci suke da shi, wasu kuma na ayyukan hannu suke da shi, wasu kuma na iya gudanar da mulki suke da shi, sannan wasu kuma karfin siyasa da ayyukan soji suke da shi...da dai sauransu.
Haka lamarin yake, don kuwa dan'Adam yakan gano iko da karfin da Allah Ya yi masa ne ta hanyar gwaji, don haka kada mutum ya wulakantar da abin da Allah Ya arzurta shi na daga karfi da kuma iko.
Sau da dama mutane sukan wofantar da kwarewa da kuma karfin tunani da kuma na aiki da Allah Ya ba su saboda yanke kauna da kuma jin gazawa. Ta hakan sai ka ga sun lalata karfin da suke da shi da kuma hana kansu hakkin da ya dace da ita da kuma hana ta damar ci gaba da kuma samun nasara.
Lalle babu shakka, yarda da kai, buri da kuma kokari sukan karfafa rai da kuma ba ta dukkan abin da take bukata wajen ci gaba da kuma gudanar da ayyukanta kamar yadda ya dace. Don kuwa dogaro ga Allah da kuma yarda da kai, mabudi ne na aiki da kuma cimma nasara a rayuwa.


1. Mizan al-Hikma na Muhammad Ri Shahri, juzu'i na 4 / (al-Sa'adah).
2. Mizan al-Hikma na Muhammad Ri Shahri, juzu'i na 3 / (al-Zilla).Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
8+1 =