Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

SABO DA SAKAMAKONSA (1)


Mu'assasar Al-Balagh


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, kana tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah Muhammadu tare da tsarkakan mutanen gidansa da kuma zababun sahabbansa.
Shi dan Adam a dabi'arsa yana da ikon yin biyayya da kuma sabo. Yana da 'yancin zaban daya daga cikin wadannan hanyoyi matukar dai ba an tilasta shi ba ne.
Sai dai shi mutum ba ya iya fahimtar falala da albarkar da ke cikin yin biyayya, face sai ya kasance ya mika kome nasa ga Allah, yana mai neman taimako da kuma shiriyarSa. Yana mai karban kiran Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma koyi da abubuwan da ya zo da su. Idan har mutum ya yi sa'ar riko da imani (Musulunci) da kuma aikata karantarwar Manzonmu, Muhammadu (a.s.), to zai sami kwan-ciyar hankali da farin ciki duniya da lahira, in kuwa ba haka ba, to zai fuskanci kunci da damuwa.
Hakika za a iya takaitar da damar da dan'Adam yake da ita wajen sabo a duk lokacin da yake riko da dokokin Musulunci, aikata umurnonin Allah da kuma kula da fidiransa (wato irin kyakkyawan yanayi da aka halicci mutum), al'ummar da yake ciki da kuma Ubangijinsa. Hakika wajen aiwatar da wannan muhimmin aiki, Musulunci ya yi matukar kokarinsa wajen shiryar da mutum zuwa ga hanya madaidaiciya kana kuma ya nuna masa yadda zai guje wa sabo. Hakan kuwa ba tare da ya kwace masa 'yancin da yake da shi na zabi da kuma ikon aikata alheri ko sharri ba.
Don haka ne, Mu'assasar Al-Balagh a burinta na shiryar da mutane take gabatar muku da wannan littafi, "Sabo da Sakamakonsa", a silsilar littattafan da ake kira da "Fahimtar Musulunci", daidai da koyarwar Musulunci. Manufa da burin yin hakan kuwa shi ne samar da mafita da kwanciyar hankali ga wannan duniya tamu mai cike da fitinu da rikice-rikice.

Mene ne Sabo?

Ana iya fassara sabo da cewa wani yanayi ne na kin yarda da kasancewa karkashin mashi'ar Ubangiji, wanda a hakikanin gaskiya, mashi'a ce ta alheri da adalci. Sannan kuma za a iya fassara shi da cewa wani yunkuri ne na dan'Adam wajen yin karen tsaye wa dokoki da ka'idojin rayuwar 'yan'Adam. Dukkan halittu an halicce su ne da wasu irin tsarurruka da haddodi da suka dace da su; wadanda saba musu haramun ne. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Kuma wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, kuma ya ketare iyakokinsa, Zai shigar da shi wuta". (Surar Nisa'i, 4:14)
Don haka, an bayyana sabo a matsayin abu mai cutarwa, wanda ya saba wa dabi'ar dan'Adam.
Su batattun mutane masu wuce haddi sun kasance suna rasa fahimtar munin wuce haddi, sannan ba sa girmama ma'ana da kimar abubuwa. Don haka ne ba sa yin mu'amala da kyawawan abubuwa, kuma suka saba wa tsarurrukan hankali da kuma mika wuya ga munanan ayyuka. A sabili da haka ne ma, Alkur'ani mai girma ya siffanta shirka - don kuwa ita ce ginshikin duk wani sabo- a matsayin fadowa daga wani waje mai tsawon gaske, inda yake cewa:
"...kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yana kamar abin da ya fado daga sama, sa'annan tsuntasaye suka café shi, ko kuma iska ta fada da shi a cikin wani wuri mai nisa". (Surar Hajj, 22: 31)
A saboda haka, sabo ya kumshi duk wani aiki da ya saba wa dokokin dabi'u na kwarai wanda shari'ar Ubangiji ta zo da shi kana lafiyayyen hankali da tsarkakakkiyar fidira wacce bata ba ta shafe ta ba ta gano shi. a koyarwar Musulunci, sabo yana nufin barin wajibai da kuma aikata abubuwan da aka haramta, sannan da barin ayyukan alheri da aikata sharri da munanan ayyuka.
A wannan zamani namu, 'yan'Adam suna fuskan-tar wahalhalu masu tsanani, saboda nuna halin ko-in-kula da suka yi dangane da abubuwan da suke hara-mun. A saboda haka ne ma, gwamnatoci daban-daban suka ba da muhimmanci mai girman gaske wajen yaki da laifuffuka da munanan ayyuka, ta hanyar amfani da duk wani karfin kimiyya da na dan'Adam da suke da shi wajen gyara al'umma don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar jama'a da kuma kasa baki daya. Bugu da kari kan samar da kyakkyawan yanayi na ci gaban al'umma. To amma duk da wannan kokari da suke yi wajen fada da munanan ayyuka, ba su sami nasarar kawar da laifuffuka da munanan ayyuka ba, face ma dai sai ci gaba suke yi.
Wadannan shirye-shirye da tsarurruka na gyara, ba su sami nasara ba ne saboda tsara su ne ba tare da la'akari da dokokin Ubangiji ba. Wadannan ka'idoji, mahanga da tsarurruka da wadan-nan gwamnatoci suka dauka a matsayin mahangar tsare-tsarensu na yaki da miyagun laifuffuka sun samo asali ne daga akidar da ta yi nisa da Ubangiji.
A dalilin haka, dukkan kwararrun wajajen bincike, dakunan kimiyya da kuma kungiyoyin fada da miya-gun laifuffuka suka gagara aikata wani abin a-zo-a-gani, don kuwa sun gagara fahimtar amfani da tasirin dokokin Ubangiji. Hakika da sun bukaci taimako daga dimbin ilimin Ubangiji kana suka yi amfani da hankali da kuwa sun gano mafita daga da yawa daga cikin matsalolinsu.

Nau'o'in Sabo

Kamar yadda aka sani ne cewa sabo shi ne bijire wa dokokin Allah da kuma barin tafarkin gaskiya da adalci, don haka ne ake ganinsa a matsayin mummu-nan al'amari wanda ya saba wa hankali. Kana kuma a dalilin haka ne ma Musulunci yake ganin duk wani aikin da ya saba wa ka'idojin kyawawan dabi'u a matsayin mummunan aiki kana kuma mai cutar da dan'Adam. A saboda la'akari da hakan, Musulunci bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayyanar da ayyuka da dabi'un da suke munana ne kuma zunubai ne:
1. Rashin aikata wajibai kamar salla, azumi, aikin hajji da dai sauransu.
2. Sabo yakan tabbata ta hanyar aikata ayyukan da aka haramta, kamar shan giya, riya, zina, jiji-da-kai, hassada, rawa da dai sauransu.
Hakika wadannan masu sabo ba su kyauta wa kansu ba ta hanyar bayyanar da kansu ga azaba da kaskanta da kuma fushin Allah.
3. Ayyukan sabon da cutarwarsu yakan shafi sauran mutane. Wadannan masu aikata sabo sukan cutar da dai-daikun mutane da kuma al'umma gaba daya ta hanyar aikata munanan ayyukan da suke janyo barazana ga zaman lafiya da kuma kwanciyar hankalin al'umma.
A bisa tsarin Musulunci, aikata munanan ayyuka kamar kisan kai, sata, cin amana, yaudara, zalunci, cuta, cin kudin ruwa, boye kayayyakin amfanin yau da kullum don ya yi tsada [1] da dai sauransu, sukan haifar da cutarwa mai yawan gaske ga ayyuka da mu'amalolin jama'a. Koda yake, a dokokin tsarin Sekula [2] , manyan munanan ayyuka kamar cin kudin ruwa, boye kayayyakin amfani, shan giya da muggan kwayoyi ba a dauke su a matsayin laifuffukan da za a iya hukumta mutum a kansu ba.
A saboda wannan dalili ne, al'ummomin da suke karkashin irin wannan tsari suke fuskantar hawa-hawan faruwan muggan laifuffuka da suke haifar da barazana ga salin tushen zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma. Inda kuma aka halalta ayyuka irin zina, luwadi, shan giya, safaran muggan kwayoyi, caca da sauransu, sannan a wasu lokuta ma ake bayyanar da su a matsayin ayyukan da aikata su ba laifi ba ne. Idan har aka yi la'akari da wadannan bayanai, za a ga cewa rundunar shedanci da kuma laifuffuka da ke cikin mutane a sake suke kana al'umma kuma suna fuskantar yaduwar zubar da jini, kashe-kashe, yake-yake da muggan cututtuka. To amma shi Musulunci a nasa bangaren ya yi iyakacin nasa kokarin wajen fadakarwa da kuma tsara al'amur-ran 'yan'Adam da kuma kirkiro shirye-shirye don rage tasirin miyagun ayyuka da kuma gabatar da dokoki da tsare-tsaren gyara wanda zai bai wa mutum da al'ummar da yake ciki damar rayuwa cikin aminci da kwanciyar hankali.

Tasirin Sabo Ga Mutum

Sabo wani irin al'amari ne da yake tare da dan'Adam, to amma yana tabbatuwa ne a duk lokacin da mutum ya zabi ya bayyanar da shi. Don haka, daga lokacin da aka bayyanar da shi, to yakan bakanta zuciyar mutum. Sannan kuma daga lokacin da zunubi da sabo suka mamaye wannan guri (zuciya), to mutum yakan rasa shaukin aikata alheri da abubuwa masu kyau, kuma zahirinsa yakan misaltu da aikata muggan ayyuka da kuma mugunta. A saboda wannan dalili, za mu ga duk mutumin da ya rasa kimarsa na dan'Adamtaka yakan yi kunnen uwar shegu da kuma nuna rashin damuwarsa kan aikata ayyukan alheri. Irin wannan mutum yakan zama kasurgumin mai aikata laifuffuka da zunubai. Alkur'ani mai girma yana bayani kan irin wannan mummunan al'amari, cewa:
"A cikin zukatansu akwai wata cuta; sai Allah Ya kara musu wata cuta, kuma suna da azaba mai radadi, saboda abin da suka kasance suna yi na karya". (Surar Bakara, 2: 10)
"A'a ha! Ba haka ba abin da suka kasance suna aikatawa dai, ya yi tsatsa a cikin zukatansu". (Surar Mudaffifin, 83: 14)
"...to, a lokacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukatansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasikai". (Surar Saff, 61:5)
"Sa'an nan kuma zukatanku, suka kekashe daga bayan wancan. Saboda haka suka zama kamar duwatsu ko mafi tsanani ga kekashewa". (Surar Bakara, 2: 74)
"To, saboda warwarewarsu ga alkawarinsu, da kafiratarsu da ayoyin Allah, da kisan su ga Anna-bawa ba da hakki ba, da cewarsu, zukatammu suna cikin rufi. A'a, Allah ne Ya yunke a kansu saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kadan". (Surar Nisa'i, 4: 155)
Daga wannan bayani na Alkur'ani, za mu fahimci cewa, an arzurta dan'Adam da hankali, hangen nesa da kuma karfin godiya. A dalilin haka, yake son aika-ta alheri da ayyukan alheri kwarai. Kana kuma yana nesantar munanan ayyuka wadanda suka bar mummunan tasirinsu a kwakwalwarsa, ta yadda bai damu da aikata duk wani laifi ba kana ya zamanto ya dabi'antu da aikata zunubai ba tare da nuna damuwa da yin nadama ba. Sannan ya zamanto wani irin mutum mai kiyayya da duk wani bangare na kyakkyawan rayuwar dan'Adam, kuma ya rasa duk wani irin nau'i na mutunci, karama, tsarkaka da dan'Adamtaka. A takaice dai, zai iya zama kasurgumin mai laifi.
Don haka, Alkur'ani mai girma ya lissafa irin mummunan tasirin da aikata sabo da zunubi da kuma ci gaba da aikata su yake haifarwa. Inda ya kawo mafi hadarinsu kamar haka:
1. Al-Zaigh : Kaucewa daga tafarki madaidaici.
2. Al-Maradh : Cuta (ciwo).
3. Al-Rain : Tsatsar zuciya.
4. Al-Kaswa : Kekashewar zuciya.
5. Al-Tab'i alal Kalb : Lullubewar zuciya.
Saboda haka, daga lokacin da mutum ya saba da aikata zunubai da sabo, to zuciyarsa takan cutu ta yadda za ta katangu daga fahimtar abin da ya dace. Zuciyar mutum takan bakanta ta yadda duk rayuwarsa za ta zamanto cikin aikata sabo da laifuffuka.
Dangane da wannan al'amari, maganganun Imam Sadik (a.s.) sun bayyana irin mummunan tasiri da sabo yake yi a kan mutunci dan'Adam, kana yana mai karin haske kan ma'anonin wadancan ayoyin Alkur'ani da suka gabata. Don haka, aka gargadi musulmi da cewa babu wani bambanci tsakanin karamin zunubi da babba, kana ya ci daga da neman gafarar Ubangiji don ya sami damar gujewa hanyar bata kuma da samun damar rayuwa wacce take cike da tsoron Allah da kuma tsarkaka.
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa:
"Babu wani abin da yake lalata zuciyar mutum kamar zunubi, zuciyarsa takan gurbata da zunubai ta yadda shi zai zamanto bawanta - sai abin da ta so zai aikata-" [3].

Dalilan Aikata Sabo

Hakika shi mai laifi (zunubi) ba ya aikata laifin face dai sai akwai wani abu ko kuma wani yanayi da yake tunkuda shi ga aikata hakan. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Shin, to, wanda aka kawata masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yana daidai da waninsa)? Saboda haka, lalle, Allah Yana batar da wanda yake so, saboda haka kada ranka ya halaka a kansu domin bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sana'antawa". (Surar Fadir, 35:8)
Duk da cewa abin da yake aikatawa ba kome ba ne, to amma shi mutum yana mai rudin kansa da cewa abin da yake aikatawa shi ne daidai. Hakika Alkur'ani mai girma ya yi bayanin irin wadannan mujirimai:
"Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi barna a cikin kasa", su kance: "Mu masu kyautatawa kawai ne! To lalle ne su, su ne masu barna, kuma amma ba su sansancewa". (Surar Bakara, 2: 11-12)
"Ka ce, ko mu gaya muku game da mafifita hasara ga ayyuka? wadanda aikinsu ya bace a cikin rayuwar duniya, alhali kuma suna zaton lalle ne su, suna kyautata (abin da suke gani) aikin kwarai". (Surar Kahfi, 18: 103-104)
Hakika, shi mutum a koda yaushe yana neman mafaka ce ga abubuwan da yake aikatawa domin ita fidiran dan'Adam ba ta kaunar mummunan abu. A dalilin haka ne ma, babu yadda za a yi ya yarda cewa abin da yake aikatawa ba daidai ba ne face ma har ya gano munin aikin nasa. Duk kuwa da cewa fidiran dan'Adam ba ta kaunar mummunan aiki, duk kuwa da cewa mummunan ayyukan suna nan, to amma sai da Musulunci ya kirkiro hanyoyi da tsare-tsaren hana aukuwan laifuffuka kana kuma ya tsaro kyawawan yanayi da zai kare dan'Adam da al'ummar da yake ciki daga fadawa cikin ramukan zunubai. A takaice dai, Musulunci ya yi amfani da duk wata hanya da yake da ita wajen ruguza abubuwan da suke haifar da aikata sabo da munanan ayyuka. Wadannan abubuwa kuwa su ne kamar haka:
1. Jahilci
2. Kaucewa ta tunani.
3. Bukatuwa da wani abu.
4. Rashin kulawa da kyawawan dabi'u da kuma rashin imani da azabar lahira.

1. Jahilci

Jahilci shi ne mafi girman al'amarin da ke hana mutum amfani da kwakwalwa da kuma fidirarsa. Ko shakka babu, duk mutumin da ya rasa cikakken ilimi da masaniya, to lalle ya rasa kwakwalwar tunani da bambance al'amurra, ya raunana ruhi da kuma kyawawan siffofinsa, kana kuma cikin sauki zai iya tunkuda kansa zuwa ga hanyar bata.
Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Ko sun riki wadansu abubuwan bautawa, baicinSa? Ka ce (Ya Muhammadu), ku kawo hujjarku. Wannan shi ne ambaton wanda yake tare da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabannina. A'a, mafi yawansu ba su sanin gaskiya, saboda haka su masu bijirewa ne". (Surar Anbiya, 21: 24)
Wannan bayani yana tabbatar da cewa ba kasafai malamai da masana suke aikata munanan ayyuka ba, koda kuwa suna cikin lalatacciyar al'umma ce. Koda yake, yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa kariya ta ainihi daga munanan ayyuka tana samuwa ne ta hanyar mallakar "Ilimi irin na Ubangiji". Domin saboda rasa irin wannan muhimmin al'amari ne, ya sanya da yawa daga cikin malamai da masana suka zamanto masu taimako da kuma shirya barna, zubar da jini, aikata laifuffuka da kuma cutar da dan'Adam. Wadannan munanan dabi'u da kuma son aikata zunubai suna wanzuwa daga wadannan malamai ne, saboda tunani da ilmummukan da babu Allah a ciki ne yake ja-gorantarsu, wanda hakika hakan wani nau'i ne na jahilci, da ke haifar da mummunar sakamako.
Hakika Manzonmu (s.a.w.a) ya yi bayanin irin wannan al'amari, yayin da yake ba da amsar tambayar da aka yi masa cewa su wane ne mafi sharrin mutane? Sai ya amsa da cewa:
"Malamai idan suka lalace" [4] .
A saboda wannan dalili ne, Musulunci ya kuduri aniyar yakan jahilci ta hanyar yada hanyoyin neman ilimi wanda hakan shi ne babban asasin gyara. Wannan babban muhimmanci da Musulunci ya bai wa ilimi ya samo asali ne daga irin i'itikadin da yake da shi na cewa rashin kyakkyawan ilimi na iya taimakawa wajen faruwar mummunan ayyuka da zunubai. Sannan kuma mallakar kyakkyawan ilimi mai amfani zai iya samar wa mutum hasken hikima da fahimta kana kuma ya taimaka masa wajen dasa imani, kaunar juna, tausayi da kyautatawa da kuma nuna rashin amincewa da duk wani nau'i na sabo.
"Ya ce, ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma amma ina ganinku, wasu mutane ne, masu jahiltar gaskiya". (Surar Ahkafi, 46: 23)
"Lalle ne kai, ba ka jiyar da matattu, kuma ba ka sa kurame su ji kiranka, idan sun juya suna masu bayar da baya. Kuma kai ba ka zama mai shiryar da dimammu daga bata ba. Ba ka jiyarwa face wanda yake yin imani da ayoyinmu. To, su ne masu sallamawa - al'amari zuwa ga Allah -". (Surar Namli, 27:80-81)
"A'a ha! Wadanda suka yi zalunci sun bi son zuciyoyinsu, ba tare da wani ilimi ba. To, wane ne zai shiryar da wanda Allah Ya batar? Kuma ba su da wadansu mataimaka". (Surar Rum, 30:29)
Hakika Alkur'ani mai girma ya siffanta wadanda suka jawo wa kansu fushin Allah da wadanda jahilci ya rufe musu ido.
Idan muka dubi cikin wadannan ayoyi na Alkur'ani, za mu iya fahimtar dalilan aikata munanan ayyuka a mahangar Alkur'ani:
Na farko, an kwatanta jahilci da cewa makanta da kurmanci ne tun da suna hana mutum yarda da gaskiya da kuma adalci.
Na biyu, an siffanta jahilci a matsayin mutuwa don kuwa yana lalata wa mutum rayuwa. Don duk wata alakar mutum da duk wani bangare na tunani da fahimta yakan lalace. Bugu da kari, Musulunci yana kwadaitar da dan'Adam wajen neman ilimi da masaniya wanda yakan bude masa hanyar shiriya da farin ciki. A saboda wannan dalili ne, Allah Ya aiko da Annabawa da Manzanni don su shiryar da mutane, ta hanyar dalilai da ilimi, zuwa ga hanya madaidaiciya.

2. Kaucewa Ta Tunani

Babu shakka, irin al'ummar da mutum ya taso a ciki da kuma tarbiyyar da ya samu, suna da matukar tasiri ga rayuwa da dabi'unsa. Domin akan haifi mutum ne a cikin mafi tsarkakakken yanayi, ta haka ne zai ci gaba da girma cikin irin yanayin da ya sami kansa a ciki, wadanda su za su tsara masa yadda halaye da dabi'unsa za su kasance.
Matukar dai mutum ya girma cikin kyakkyawan yanayi da kuma tsarkakan al'umma, to ruhinsa yakan sami wani karfi da kuma kulawa wanda ka iya bashi daman samun daukaka da kuma komawa zuwa ga alheri da kyawawan dabi'u. A takaice dai, zai iya samun damar isa ga babban buri da manufar rayuwarsa, wato biyayya da kuma mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki. A daya bangaren kuma, mutumin da ya rasa tsarkakakken yanayi da kuma tarbiyya mai kyau, yakan wayi gari cikin son kai, munanan ayyuka, rashin da'a da kuma rashin sanin ya kamata, wanda sakamakon hakan shi ne samar da wani irin dimaucaccen mutum wanda bai san ya kamata ba. Inda daga karshe mutum yakan zama bawan kyalkyale-kyalkyalen duniya da son zuciyarsa ta inda zai zamanto ya dabi'antu da aikata kisan kai, sace-sace, zinace-zinace, yaudara, shaye-shaye da kuma nisantar kyawawan dabi'u.
A saboda wannan dalili ne, Alkur'ani mai girma ya yi dubi cikin wadansu masu aikata zunubi kana ya nuna cewa addini, wato Musulunci, shi ne hanyar tsira. Sannan kuma mummunar dabi'a, wani takai-taccen yanayi ne na ruhi wanda za a iya magance shi ta hanyar kawar da irin munanan yanayin da yake ciki don a samar wa ruhi da kwakwalwa mutum abubuwan da suka dace da su. Hakika ayoyin Alkur'ani sun bayyanar da irin wadannan masu wuce haddi ta hanyar bayyanar da mummunan tunaninsu. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
"Sa'an nan kuma a bayansu Muka aika Musa da Haruna zuwa ga Fir'auna da mashawartansa, tare da ayoyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutane masu laifi". (Surar Yunus, 10: 75)
"A cikin zukatansu akwai wata cuta; sai Allah Ya kara musu wata cutar, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna yi na karya". (Surar Bakara, 2: 10)
"Kuma idan an karanta ayoyinmu a gare shi, sai ya juya baya, yana mai girman kai, kamar dai bai saurare su ba, kamar dai akwai wani danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushara da azaba mai radadi". (Surar Lukman, 31:7)
"Kuma suka yi musunsu, alhali zukatansu, sun natsu da su, domin zalunci da girman kai. To, ka dubi yadda karshen mabarnata ta kasance". (Surar Namli, 27:14)
"Idan aka karanta masa ayoyinMu, sai ya ce tatsuniyoyin mutanen farko ne". (Surar Mudaffifina, 83: 13)
"Za ni karkatar da wadanda suke yin girman kai a cikin kasa ba da wani hakki ba, daga ayoyiNa, kuma idan sun ga dukkan aya, ba za su yi imani da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiri-ya, ba za su rike ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar bata, sai su rike ta hanya. Wancan ne, domin lalle ne su, sun karyata da ayoyinMu, kuma sun kasance, daga burinsu gafilai". (Surar A'arafi, 7: 146)
Hakika daga wadannan bayanai na Alkur'ani, za mu iya fahimtar wani muhimmin al'amari, shi ne kuwa cewa wadannan batattun mutane, son zuciya da alfahari ne yake rudinsu. Don haka ne zukatansu suka kekashe, ba sa iya tunani mai kyau da fahimtar al'amurra. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
"To, don me masu hankali ba su kasance daga mutanen karnonin da suke a gabanninku ba, suna hani daga barna a cikin kasa? Face kadan daga wanda muka kubutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma wadanda suka yi zalunci suka bi abin da aka ni'imatar da su a cikinsa, suka kasance masu laifi". (Surar Hud, 11: 116)
Hakika Alkur'ani mai girma ya ta kawo wadannan bayanai ne don ya shiryar da dan'Adam zuwa ga hanya madaidaiciya, hakan kuwa don amfani 'yan'Adam da kuma daukakan gaskiya da adalci ne.
"Domin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya bata karya, kuma koda masu laifi sun ki). (Surar Anfali, 8: 8)

3. Bukatuwa

Hakika tabbataccen al'amari ne cewa biyan bukatan dan'Adam na duniya ako da yaushe yana daga cikin dalilan da suke kawo kyakkyawa kana tsarkakakkiyar rayuwa. Rahsin hakan kuwa na iya sa mutum ya gagara kare kansa daga fadawa cikin aikata munanan ayyuka da kuma laifuffuka. Don haka ne ma, Musulunci ya ba da gagarumin muhimmanci ga abubuwan bukatuwa na rayuwa ta hanyar tsara dokoki da ka'idoji wadanda za su taimaka wa mutum wajen gudanar da kyakkyawan rayuwa cikin farin ciki da daukaka.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tabbatar da wannan al'amari, yayin da yake cewa:
"Babu abin da yafi taimakawa ikhlasi da gaskiya mutum kamar wadata" [5].
Sannan kuma yana cewa:
"Wadatar da take kare ka daga aikata zalunci ita ta fi fakircin da ke janka zuwa sabo" [6].
Kana kuma an ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yayin da yake yabon Ubangiji, yana cewa:
"Ka albarkace mu da biredi (abinci), kada Ka raba tsakaninmu da shi, idan har babu abinci, to ba za mu sami daman yin salla, azumi da sauran wajibai ba" [7].
Don haka, Musulunci ya ba da matukar muhim-manci ga wannan al'amari ta inda har ya bayyana cewa babu laifi ga mutumin da ya aikata haramun yayin da yake cikin talaucin da rashin aikata wannan aiki zai kai shi ga rasa ransa. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"....to, wanda aka matsa, wanin dan tawaye, kuma banda mai zalunci, to, babu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin kai". (Surar Bakara, 2: 173)
Daga wannan bayani, za mu fahimci cewa wuce haddin dan'Adam ya samo asali ne daga rashin wadata. A takaice dai, a wasu lokuta, mutum yakan aikata zunubai a bisa tilas. A bisa haka, ana iya cewa al'ummomin da ba na Musulunci ba, ba su yi adalci wa dan'Adam ba don kuwa an bar shi ba tare da kare shi daga barazanar talauci, kuma aka raba shi daga ni'imar kyakkyawar rayuwa da kuma ilimi mai amfani. Hakika babu wani dalilin da za a tuhimci mutane kana a yanke musu hukumci kan aikin da suka aikata cikin tilas (ba da son ransu ba).

4- Rashin Kulawa da Kyawawan Dabi'u Da Rashin Imani Da Azabar Lahira:

A duk lokacin da mutum ya rasa shaukin kyawa-wan dabi'u da rashin sanin ya kamata kana ya hadu da rashin imani da Allah da akidar sakamako da azaba bayan mutuwa, to jure wa rashin aikata zunubi zai yi masa wuya. Abu mai muhimmanci a wannnan al'amari, shi ne imani da Allah, Masanin abin da ke boye (gaibi), wanda Shi ne mabubbugar duk wani alheri da albarka kana Mai kula da duk wasu halaye na dan'Adam. Daga karshe, hakika Musulunci ya ba da muhimmanci mai girman gaske kan ilimin akida da kuma wani tsari da zai kula da rayuwar mutum ta bayyane da ta ruhi.


1. A baya-bayan nan wasu tsarurrukan siyasa sun dauki boye kayayaki a matsayin laifi wanda ake hukumta mutane a kai.
2. An fassara tsarin "Sekula" da cewa wasu tsarurruka ne wadanda dan'Adam ya kirkiro ba tare da la'akari da dokokin Allah ba.
3. Usul al-Kafi na Kulayni, juzu'i na biyu, shafi na 268, bugu na uku.
4. Tuhaf al-Ukul na al-Harani, shafi na 36, bugu na biyar.
5. Usul al-Kafi na Kulaini, juzu'i na 5, shafi na 71.
6. Kamar na sama, shafi na 72.
7. Kamar na sama, shafi na 73.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
3+5 =