Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

SABO DA SAKAMAKONSA (2)


Mu'assasar Al-Balagh


Yadda Musulunci Ya Magance Matsalar Sabo

Saboda la'akari da kasantuwan sabo na daga cikin ayyukan da suke ruguza al'umma, Musulunci ya yi amfani da duk wani karfi da yake da shi wajen tsige tushen wannan bala'i, don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin al'umma. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Ya mutanen littafi! Lalle ne, ManzonMu ya je muku, yana bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kuna boyewa da littafi, kuma yana rangwame daga abu mai yawa. Hakika, wani haske da wani littafi mai bayyanawa ya je muku daga Allah. Da shi, Allah Yana shiryar da wanda ya bi yardarSa zuwa ga hanyoyin aminci, kuma Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininSa, kuma yana shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya". (Surar Ma'ida, 5: 15-16)
Musulunci ya yi hakan ne saboda la'akari da ka'idojin da suka dace da ci gaban dan'Adam da al'ummar da yake ciki, don kuwa Musulunci ya kasance addini ne na ilimi da kuma shiryarwa irin ta ruhi. Kana kuma, Alkur'ani a fili ya bayyana cewa manufar Musulunci ita ce shiryar da dan'Adam zuwa ga hanya madaidaiciya ta hanyar fitar da shi daga duhu zuwa ga haske don ya samu damar rayuwa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. A takaice dai don mutum ya sami kyakkyawan raywua da kwanciyar hankali, Musulunci ya dauki wasu matakai da tsare-tsare don ruguza kangin sabo da rashin biyayya, sannan kuma ya bude kofofin biyayya da kuma mika wuya ga gaskiya da kyawawan al'amurra. Daga cikinsu, akwai:

1- Yada Ilmi da Masaniyya da kuma Yakar Jahilci da Camfe-Camfe

Don ba wa mutum daman kiyaye shu'uri, tunani da mutuncinsa, Musulunci ya jaddada muhimmancin amfani da wa'ayi da kuma kwakwalwa. Alkur'ani mai girma, dangane da hakan, yana cewa:
"….Malamai kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa….". (Surar Fadir, 35: 28)
Dangane da hakan ma, Imam Musa al-Kazim (a.s.) yana cewa:
"Hakika an halicci mutane ne don su yi da'a wa Allah. Ceto ba ya yiyuwa ba tare da biyayya ba, kuma biyayya ba ta yiyuwa sai da ilimi" [1].

2- Imani Da Adalcin Allah Da Kuma Sakama-kon Lahira.

Wannan al'amari ya kasance daya daga cikin shika-shikan akidar Musulunci, kuma an yi bayanin wannan al'amari cikin Alkur'ani mai girma:
"To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra na alheri, zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)
Saboda karfafa wannan tabbatacciyar akida, mumini yakan sadaukar da kansa ga kyawawan dabi'u da kuma guje wa munana. Wadannan ayoyi na Alkur'ani mai girma masu zuwa, sun yi bayanin wannan lamari:
"Kuma ku tsayar da su, lalle su, abin tambaya ne". (Surar Saffati, 37: 24)
"Kuma kowane mutum Mun lazimta masa abin rekodinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a ranar lahira da littafi wanda zai hadu da shi budadde". (Surar Isra', 17: 13)
Hakika daga lokacin da mutum ya damfaru da wannan akida, to zai fahimci dadin da ke cikin biyayya da kuma aiki daidai da dokoki da ka'idojin kyakkyawan rayuwa wacce take cike da farin ciki da daukaka. Ko kuma ana iya cewa, ayyuka da daukakan dan'Adam zai samu tsarkaka.
"….kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku....". (Surar Bakara, 2: 235)
"Allah Ya san yaudarar idanu da abin da kiraza ke boyewa". (Surar Ghafir, 40: 19)

3- Biyan Bukatun Dan'Adam Da Kuma Magance Talauci.

A koda yaushe wannan babban al'amari yana nuna irin kokarin da Musulunci yake yi wajen kawar da tasirin tsananin talauci. Don kuwa, Musulunci ya sanya biya wa dan'Adam bukatunsa na yau da kullum a matsayin daya daga cikin wajibansa, ta hanyar kirkiro da harajoji na wajibi kamar su zakka, khumsi (daya bisa biyar na kudin shigan mutum) don kubutar da 'yan'Adam daga barazanar talauci. Hakika tun farko halittar dan'Adam aka kafa wadannan wajibai. Dangane da hakan Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Lalle ne ka samu, ba za ka ji yunwa ba a cikinta, kuma ba za ka yi tsiraici ba". (Surar D.H., 20: 118)
"Saboda haka, sai su bauta wa Ubangijin wannan gida (Ka'aba). Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsoro". (Surar Kuraish, 106: 3-4)

4- Kariya ta Shari'a

Daga cikin muhimman siffofin sakon Musulunci shi ne cewa yana daukan kwararan matakan tsaro da kuma kariya daga aikata zunubi kafin hukumta wanda ya aikata shi, hakan kuwa ta hanya tsara dokoki da ka'idojin da za su tabbatar da tsaro ga dan'Adam. Hakika Musulunci ya haramta kisan kai, sata da yin zina, to amma bai tabbatar da hakan ba tare da ya tsige duk wasu munanan hanyoyi (da suke janyo hakan) ba, kamar giya, caca da hotuna da fila-filan batsa da dai sauransu.

5- Kange Mutane da Kuma Tsarurrukan Gyara

An siffanta mutum da cewa shi wata halitta ce wanda halaye da mu'amalarsa da sauran 'yan'uwansa yana da wani irin gagarumin tasiri ga dabi'unsa, koda yake irin kaskantar da shi da mutane za su yi a duk lokacin da ya saba wa wata ka'ida ta kyawawan dabi'u za ta iya kaskantar da shi ya zama ba kome ba. A sakamakon haka, zai yi kokarin boye kansa daga mutane don ya tserar da kansa daga cin mutuncin mutane.
Don haka, an halitta wa mutum wannan mika wuya na fidira ce don ya yi daidai da hikimar Ubangiji wacce ta kasance take amfanar da mutum wajen kaunar dokoki da adalci. Bayan da ya wajabta wa mutum aikata kyawawan dabi'u da kuma hana shi aikata munana, Musulunci ya samu nasara wajen ware wadannan mutane (masu sabo) da niyyar sanya su cikin kunci da jin kunya don ya motsar da fidirar alheri da daukaka ta inda za su sami sauyin ra'ayi kan aikata sabo.
An ruwaito Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa:
"A duk lokacin da wani ya kawo maka zancen wani, to ka ce masa, idan har kana son ka zauna da mu, to dole ne ka bar aikata hakan, idan har bai bari ba, ya zama dole ku kore shi" [2].

6- Tuba Da Kuma Fatan Gafarar Ubangiji.

Tuba wata hanya ce da Allah, cikin ni'ima da rahamarSa, Ya arzurta bayinSa da ita don su sami mafaka daga zunubansu. Allah Yana gaya wa masu barna cewa:
"Ka ce: (Allah Ya ce), Ya bayiNa wadanda suka yi barna a kan rayukansu! Kada ku yanke kauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Na gafarta zunu-bai gaba daya. Lalle Shi, Shi ne Mai gafara, Mai jin kai". (Surar Zumar, 39: 53)
Daga wannan bayani, za mu fahimci cewa tuba ta kasance tana da tasiri wajen dawo da mutum zuwa ga fidirarsa, kana tana ba shi daman tuntuni cikin zunubansa da suka gabata da kuma daura aniyar aikata alheri da barin sabo. A saboda tunanin gafarar Ubangiji da sabuwar hanyar da ya kama, shi wannan mai tuba, saboda tasirin wannan sabon yanayi da ya samu, zai sami karfin gwuiwa da kyakkyawan rayuwa.

Karfin Mulki (Shari'a) Da Kuma Tarbiyyantarwa

Hakika a fili yake cewa hukumta masu laifi zai kare su daga ci gaba da wannan mummunan aiki nasu don su kare mutuncinsu. Alkur'ani mai girma ya yi bayanin muhimmancin hukumta masu laifi:
"Kuma kuna da rayuwa a cikin kisasi, ya ma'abuta hankula; tsammaninku, za ku yi takawa". (Surar Bakara, 2: 179)
Dangane da wannan al'amari Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Abubuwan da doka (hukuma) za ta iya hanawa ta hanyar mai mulki, ba zai yiyu ga Alkur'ani ya hana ba" [3].
Bayan da aka riga aka gano tasirin hukumci wajen hana aikata laifi, Musulunci ya kirkiro haddi (hukumci) a matsayin wata muhimmiyar hanya wajen hana aikata laifuffuka a lokacin da ilimi da tarbiyya suka gagara samun nasara. Don haka, gudanar da hukumce-hukumce tare da kira ga kyawawan dabi'u sun kasance mafi dacewan al'amari wajen gyaran al'umma.

Sabo Da Kuma Sakamako

A bisa mahangar Musulunci, ana ganin mutum a matsayin shugaban dukkan halittu duniya. Don haka duk ayyukansa, wadanda suka dace da wadanda ba su dace ba, sun kasance a karkashin tasirin "Ka'idar Zamantakewa", wanda ke nuna cewa ayyuka da dabi'un dan'Adam, kyawawa ko munana, sun cancanci sakamako ku azabar da ta dace da su. Idan har aka rasa wannan ka'ida, wato ka'idar sakamako, to kokari da kuma ayyukan mutum za su rasa wani amfani kana kuma kimar rayuwa za ta kasance cikin rudu, bugu da kari kuma adalcin Ubangiji zai zamanto ba shi da wata ma'ana. Bisa la'akari da cewa dan'Adam halitta ce mai tsananin son kanta, don haka Musulunci sai ya yi amfani da wannan so wajen tsara dokoki da ka'idojin ukuba. Don kuwa wadannan dokoki za su hana shi jin dadi da walwala da kuma sanya shi cikin wahala, to hakan yakan sa shi a wasu lokuta ya nesance su.
Haka nan kuma, Allah Ya tsara azabobi wadanda ayoyin Alkur'ani suka bayyana su a matsayin sakamakon ayyukan dan'Adam da kuma tabbatar da adalci da hikimar Ubangiji. Bisa dubi cikin bayanan Alkur'ani kan azabtarwa, za mu iya gani wadannan abubuwa, kamar haka:
(1)- Azabtarwa a matsayin "Ka'ida ta Dabi'a" wanda suke da alaka ta kurkusa da sauran ka'idoji na ayyukan dan'Adam da na al'umma. Alkur'ani mai girma yana bayanin wannan al'amari kamar haka:
"...lalle, idan wani mai gargadi ya zo musu, tabbas za su kasance mafi shiryuwa, daga dayan al'ummomi. To, a lokacin da mai gargadi ya je musu, bai kara su da kome ba face gudu. Domin nuna girman kai a cikin kasa da makircin cuta. Kuma makirci na cuta ba ya fadawa face a kan mutanensa. To, shin, suna jiran (wani abu ne) face dai hanyar (kafiran) farko. To, ba za ka sami musanya ba ga hanyar Allah. Kuma ba za ka sami juyarwa ba ga hanyar Allah. Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin kasa, domin su duba yadda karshen wadanda suka gabace su ba? Alhali kuwa sun kasance mafifita karfi daga gare su? Kuma Allah bai kasance wani abu na iya rinjayarsa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kasa. Lalle Shi ne Ya kasance masani, Mai ikon yi". (Surar Fadir, 35: 42-44)
"Kuma, hakika, mun halakar da al'ummomi daga gabanninku, a lokacin da suka yi zalunci, kuma Manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu, amma ba su kasance suna imani ba. Kamar wannan ne, muke sakawa ga mutane masu laifi. Sa'an nan kuma muka sanya ku masu mayewa a cikin kasa daga bayansu, domin mu ga yaya kuke aikatawa". (Surar Yunus,10: 13-14)
"Kuma wani Annabi bai je musu ba face sun kasance, game da shi, suna masu yin izgili. Sai Muka halakar da wadanda suke su ne mafiya karfin damka daga gare su. Kuma abin misalin mutanen farko ya shude". (Surar Zukhruf, 43: 7-8)
"Kuma babu abin da ya hana mutane su yi imani a lokacin da shiriya ta zo musu, kuma su nemi gafara daga Ubangijinsu, face hanyar farko ta je musu ko kuma azaba ta je musu nau'i-nau'i". (Surar Kahfi, 18: 55)
Bisa wadannan kalmomi na Allah, an bayyana azabtarwa a matsayin tabbataccen sakamakon aiki wanda ke tabbatuwa a duk lokacin da aka samar da abubuwan da suke tabbatar da shi, kamar lalacewa, zalunci, cin mutunci da sauransu.
(2)- Sau da dama azabtarwa tana ta'allaka ne da wani takamammen aiki, ba wai kawai wani al'amari ne da aka dora wa raunanan mutane tare da wani dalili ba.
(3)- Azabatarwa tana da alaka ta kurkusa da adalcin Ubangiji wanda hakan yana nuna cewa Allah ba zai bar azzalumai su tafi haka kawai ba tare da yi musu azaba ba. Sannan su kuma wadanda aka zalunta a dauko musu fansa. Alkur'ani mai girma ya na cewa:
"Yana mai karkatar da sashensa domin ya batar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yana da wani wulakanci a duniya, kuma Muna dandana masa azabar gobara a ranar lahira. (A ce masa) wancan azaba saboda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah Bai zama Mai zalunci ga bayinSa ba". (Surar Hajj, 22: 9-10)
4- Alkur'ani mai girma ya bayyana nau'o'i hudu na irin azabar Ubangiji:
(A)- Azabtarwa irin ta kotu
(B)- Azabtarwa irin ta al'umma
(C)- Azabtarwa irin ta Ubangiji
(D)- Azabtarwa irin ta Lahira

(A)- Azabtarwa Irin Ta Kotu
Wannan ya hada da duk wadansu matakai na hukumce-hukumce, ka'idoji, dokoki da cin tara wadanda ake gudanarwa a dokokin laifuffuka (a kotuna) kamar su hukumcin kisa, tilasta biyan hakki da kuma yanke hukumci.

(B)- Azabtarwa Irin Ta Al'umma
Irin wannan azabtarwa tana faruwa ne a sakamakon bijirewar mutane ga sakon Ubangiji da kuma aikata ayyukan sabo wanda ke kawo wahalhalu, bakin ciki da bala'i na gaba daya. Wannan tabbatac-cen bala'i yana faruwa ne a sakamakon kauce wa hanya madaidaiciya wacce Ubangiji Ya zaba. Inda daga karshe, azabobi kala-kala za su sauko wanda za su iya sa dukkan al'umma cikin halin kaka-ni-kayi. Saboda haka ne, wasu ayoyin Alkur'ani da hadisai suka tabbatar da faruwar irin wadannan azabobi a duk lokacin da mutane suka kauce wa hanya madaidaiciya kana suka ci gaba da aikata munanan ayyuka. Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
"Ka ce: Shi ne mai iko a kan ya aika da wata azaba a kanku, daga bisanku, ko kuwa daga karkashin kafafunku, ko kuwa Ya gauraya ku kungiyoyi, kuma Ya dandana wa sashenku masifar sashe. Ka duba yadda Muke sarrafa ayoyi, tsam-maninsu suna fahimta".(Surar An'am, 6: 65)
"Barna ta bayyana a cikin kasa da teku, saboda abin hannayen mutane suka aikata. Domin Allah Ya dandana musu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su komo". (Surar Rum, 30: 41)
"Kuma Allah Ya buga misali, wata alkarya ta kasance amintacciya, natsattsiya, arzikinta yana je mata a wadace daga kowane wuri, sai ta kafirta da ni'imomin Allah saboda haka Allah Ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro, saboda abin da suka kasance suna sana'antawa". (Surar Nahli, 16: 112)
"Kuma lalle ne, hakika, mun kama mutanen Fir'auna da tsananin shekarun fari da nakasa daga 'ya'yan itace, tsammaninsu suna tunawa". (Surar A'arafi, 7: 130)
Dangane da hakan kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Alamar yardar Ubangiji ga bayinSa shi ne adalcin shuwagabanninsu da kuma saukin kayayyaki (a kasuwa), kana kuma rashin yardarSa, ita ce zaluncin shuwagabanninsu da kuma tsadar kayayyaki" [4].
"Duk yadda kuka kasance, za a mulke ku".
Sannan kuma yana cewa:
"A duk lokacin da lalatattun mutane suka zama masu mulki, kuma Dagattansu suka zamanto marasa mutunci, sannan kuma ake girmama fasikai, to su saurari saukar bala'i" [5].
Sannan kuma yana cewa:
"Muminai suna cikin wahalhalu har sai an gafarta musu dukkan zunubansu".
Imam Ali (a.s.) yayin da yake shawartar 'ya'yansa, yana cewa:
"Kada ku taba barin umurni da kyawawan ayyuka da kuma hani da munana, domin in kuka yi haka, to mafi sharrin al'ummarku za su mulke ku, kuma ba za a amsa muku duk salloli da addu'oinku ba" [6].
An ruwaito Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa:
"Allah Ya aika da daya daga cikin AnnabawanSa zuwa ga mutanensa kana Ya umurce shi da ya ce musu, babu wasu mutanen wata alkarya wadanda suka kasance suna Min biyayya, face sai sun arzurta da ni'imomiNa. Amma a duk lokacin da suka rabu da hanyaTa, to Zan bar su su wahala. Kana babu wasu mutanen wata alkarya da suka kasance masu sabo, face sai sun fuskanci fushiNa, amma a duk lokacin da suka komo ga tafarkiNa, to Zan bar su su amfana da ni'imomiNa. Sannan kuma ka gaya musu cewa rahamaTa ta gabaci fushiNa, don haka kada su yanke kauna, domin babu wani zunubi, kome girmansa da ba Zan iya gafarta shi ba. Kana ka gaya musu cewa, kada su sa kansu cikin fushiNa, kana kada su wulakanta salihan bayiNa, don kuwa Zan saukar musu da azabaTa" [7].
Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) din dai yana cewa:
"Hakika wani daga cikinku zai kasance mai yawan tsoron mahukunta, hakan kuwa saboda zunubansa ne, don haka sai ku yi iyakacin kokarinku wajen nisantar aikata zunubi, sannan kuma ku nisanci son zukatanku" [8].
Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) yana cewa:
"A duk lokacin da al'umma suka kirkiro wasu zunubai a cikin rayuwarsu wadanda da ba sa aikatawa, a sakamakon haka, Allah Zai saukar musu da bala'o'in da ba su taba saninsu ba" [9].

Daga wadannan bayanai da maganganu za mu iya fahimtar cewa:
1. Ayyukan mutum nakan kansa, na al'ummance da kuma na addinance, suna da alaka ta kurkusa da ka'idojin dabi'a wadanda su ne suke tabbatar da tafarkin haduwar al'amurran dan'Adam da sauran muhimman al'amurra.
2. Wannan haduwa, idan har aka yi ta a kan karfafaffen asasi, zai iya ba wa mutum ci gaba a cikin rayuwarsa, idan kuwa ba haka ba, to mutum ba zai sami kome ba, face mummunan sakamako, rudani da kuma wahalhalu wanda hakan ita ce bayyananniyar azabar Ubangiji.
Hakika a duk lokacin da mutane suka zamanto sun lalace, kana suka mika wuyansu ga munanan ayyuka, to ba za su taba tsira daga kasancewa a karkashin mulkin zalunci da kuma rayuwa cikin kaskanci saboda yin wofi da suka yi da ka'idojin Musulunci.

(C)- Azabtarwa Irin Ta Ubangiji
Wannan ita ce mafi girman dukkanin azabobi. Alkur'ani mai girma ya yi cikakken bayani kan tarihin mutane da al'ummomi da suka bar hanya kana suka ci gaba da aikata munanan ayyuka da kuma saba wa umurni da koyarwar Annabawa da Manzanni. Inda a sakamakon haka, Allah Ya saukar musu da azabarSa a bangaren guda a matsayin sakamakon abubuwan da suka aikata, sannan a daya bangaren kuma a matsayin hanya mafi dacewa ta gina rayuwar dan'Adam a kan tabbataccen asasi na takawa da kuma farkar da kwanyar dan'Adam ta nadama da tuba wanda ke sanya mutum ya dawo zuwa ga madaidaiciyar hanya. Alkur'ani mai girma yana cewa:
"Barna ta bayyana a cikin kasa da teku, saboda abin da hannayen mutane suka aikata. Domin Allah Ya dandana musu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su komo". (Surar Rum, 30: 41)
"Ka ce: Shi ne mai iko a kan ya aika da wata azaba a kanku, daga bisanku, ko kuwa daga karkashin kafafunku, ko kuwa Ya gauraya ku kungiyoyi, kuma Ya dandana wa sashenku masifar sashe. Ka duba yadda Muke sarrafa ayoyi, tsam-maninsu suna fahimta". (Surar An'am, 6: 65)

(D)- Azabtarwa Irin Ta Lahira
Alkur'ani mai girma bai taba yin cikakke da kuma karin bayani sosai kamar yadda ya yi yayin bayanin rayuwa a ranar lahira ba.
"Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to yana da goma din misalinsa. Kuma wanda ya zo da mugun aiki guda, to ba za a saka masa ba face da misalinsa. Kuma su ba a zaluntar su". (Surar An'am, 6: 160)
"To, ya ya idan mun tara su a yini wanda babu shakka a cikinsa, kuma aka cika wa kowane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhali kuwa, su ba za a zalunce su ba?". (Surar Ali Imrana,3: 25)
"Domin Allah Ya saka wa kowane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah mai gaggawar hisabi ne". (Surar Ibrahim, 14: 51)
"....to, wane ne mafi zalunci daga wanda ya karyata game da ayoyin Allah, kuma ya hinjire daga barinsu? Za mu saka wa wadanda suke hinjirewa daga barin ayoyinmu da mugunyar azaba, saboda abin da suka kasance suna yi na bijerewa". (Surar An'ami, 6: 157)
"Suna da wata shinfida daga jahannama kuma daga samanu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke saka wa azzalumai". (Surar A'arafi,7: 41)
Idan muka yi dubi cikin irin wannan siffantawa, za mu iya fahimtar cewa wannan takaitacciyar duniya wata gada ce ta zuwa lahira. Hakika ma dai lahira wani ci gaba ne na wannan duniya wacce ta kasance rayuwa ce wacce ba ta da karshe. A bisa bayanin Alkur'ani, mutum da ayyukansa a wannan duniya yana wakiltan farkon bangaren rayuwa ne; daya bangaren kuwa rayuwar lahira, wanda yake ci gaba ne na wannan rayuwa, ne yake wakiltarsa.
"To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra na alheri, zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)
A bisa wannan bayani, za mu fahimci cewa ranar lahira, ita ce ranar da za a zo da ayyukan mutum don tantancewa da kuma yin sakamako. Dangane da hakan, Sheikh Raghib Isfahani ya na cewa:
"Sakamako yana bukatuwa da abin da ya yi daidai da shi, in alheri to alheri, in kuwa sharri, to sharri, ana cewa an saka masa kan kaza da kaza. Allah Ya na cewa: "Sakamakon mummunan aiki, shi ne mummuna kamar sa" [10].
Alkur'ani mai girma ya yi cikakken bayani kan akidar sakamako:
"....Kuma wanda ya zo da mugun aiki guda, to ba za a saka masa ba face da misalinsa. Kuma su ba a zaluntar su". (Surar An'am, 6: 160)
Hakika, wannan ka'ida ta sakamako wata babbar alama ce na adalcin Ubangiji da kuma kamalarSa. Daga karshe, ka'idar "Adalcin Ubangiji" ta kumshi tasirin akida, dabi'a da na ruhi ga dan'Adam.
1. Alakar dan'Adam da MahaliccinSa ta ginu ne a kan karfafan imani kana kuma dukkan ayyukansa, kyawawa da munana, Allah ne Zai yi masa hukumci.
2. Mutumin da ya yi imani da azabar Ubangiji da kuma ka'idar sakamako, to zai nesanci aikata munanan ayyuka wadanda su ne ummul aba'isin din fadawarsa cikin rudu da wahala.
Don haka, bayanin cewa ya kamata dan'Adam ya sanya muhimmancin wadannan ka'idoji a zuciyarsa, ya zamanto wani share fage ne na kokarin dan'Adam na gina kyakkyawa kana tsabtatacciyar rayuwa wacce take cike da kwanciyar hankali da daukaka.
Hakika idan aka rasa sakamako (azabtarwa), to daidaituwar alaka da ke tsakanin aiki da kuma saka-makonsu zai jirkita matukar dai ana aikata sabo, kana kuma za a rasa kimar abubuwa sannan kuma hasken adalci zai bace a cikin rayuwa.

ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMIN1. Tuhaful Ukul na Al-Harani, shafi na 289.
2. Wasa'il al-Shia na Hur al-Amili, juzu'i na 11, shafi na 410, bugu na biyu.
3. Hadisin Kudsi.
4. Usul al-Kafi na Kulayni, juzu'i na 5, shafi na 162.
5. Tuhaful Ukul na Alharani, shafi na 25.
6. Kamar na sama, shafi na 136.
7. Usulul Kafi na Kulaini, juzu'i na 2, shafi na 274.
8. Kamar na sama, shafi na 275.
9. Kamar na sama.
10. Almufradat fi gharibil Kur'an na Raghib Isfahani, shafi na 92.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+5 =