Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

IMAM AYATULLAH RUHULLAH AL-MUSAWI AL-KHUMAINIRanar talata, biyar ga watan Yunin nan ne ya dace da kewayowar shekaru goma sha takwas da wafatin Imam Ayatullah Ruhullah al-Musawi al-Khumaini, ja-goran juyin-juya-halin kasar Iran. Imam Khumaini (Allah Ya girmama matsayinsa) ya koma ga Mahaliccinsa ne a ranar 5/5/1989, bayan ya gabatar da wasu manyan hidindimu da miliyoyin mutane ke dauka a matsayin gudunmawa ga addinin Musulunci da dan Adam baki daya.
Tunawa da wannan babban mutum a irin mummunan halin da duniyar dan Adam da kasashen Musulmi suke ciki a yau ya zama dole; wannan kuwa saboda nazari a kan abubuwan da ya shimfida ne a fagagen karantarwarsa da ayyukansa, wadanda suke kunshe da magungunan matsalolin al'umma da wadanda ake zalunta a duniya baki daya.
Duniya ta san Khumaini ne da juyin-juya halin da ya ja-goranta, wanda ya haifar da gwamnatin Musulunci a kasar Iran, abin da ya kawo karshen tsohon matsayin da kasar ke kai na zama sansanin hukumomin leken asirin kasashen Ingila da Amurka da Isra'ila, da kasancewa cibiyar aiwatar da muradun 'yan mulkin-mallaka masu wawure dukiyoyin al'ummu masamman a yankin gabas ta tsakiya mai tarin arzikin bakin gwal (man fetur). Manazarta da masu bin diddigin lamurra sun fi mayar da hankali a kan wannan bangare na tarihin wannan babban mutum, ba tare da kulawa da abubuwan da suka kewaye rayuwarsa kuma suka yi tasiri a kan kudurorinsa da matakan da ya rika dauka ba. Wannan ya sa na fahimci mahimmancin rubuta wani abu –komai kasawarsa- a kan bangarorin da suka share fagen wancan babban aiki da kowa ke iya ganinsa daga rayuwar Imam Khumaini, don masu karatu su san cewa ba haka kawai abubuwan da suka haifar da irin kafiyar Imam da kangarewarsa ga manyan 'yan kama-karya na duniya da shimfida kakkarfar gwamnatin Musulunci da ta ci gaba da wanzuwa a kan wannan tafarki na 'yanci da dogaro da kai da ya kirkira suka kasance ba. Maimakon haka nagartaccen shiri da karfafan asasai na Musulunci ne suka samar da irin wannan Mujaddadi da ya sauya tafiyar duniya da tunanin miliyoyin jama'a a karni na ashirin/ashirin da daya; karnin ilimi da wayewa, karnin bunkasar kimiyya da fasaha.

A Matsayin Dalibi

Imam Kumaini bai yi wa ayyukan addini shigan-burtu ba, sai da ya tanaji kansa a ilmance da tarbiyya. Kai! a sama da shekaru tamanin din da Imam ya share yana ayyukan addini, gwagwarmayar kafa gwamnatin Musulunci ba ta lashe kashi daya bisa ukun shekarun ba! Domin ya fara wannan aiki ne kai tsaye a shekara ta 1963; ka ga idan aka lissafa haka zuwa shekarar da ya rasu (1989) za mu ga shekaru ashirin da shida ya share yana harkokin siyasa da gwamnati. Wannan na nufin ya share kusan shekaru sittin yana harkokin ilimi –tarbiyya da karatu da karantarwa. Babu mamaki nasarar da ya samu ta kai yadda muke shaida ta a yau!
Da farko dai Imam dan malamai ne kuma jikan malamai. Kuma gidansu ya shahara tuntuni da ilimi da takawa da jihadi. Mahaifinsa shi ne Ayatullahi Sayyid Mustafa al-Musawi, ya kasance Mujtahidi (wanda ya kai kololuwa a ilimin furu'a ta yadda ba ya bukatar fatawa daga wani malami sai dai shi ya bayar). Mahaifiyarsa, Sayyida Hajara, 'yar gidan malamai ce; domin jika take ga marigayi Ayatullahi al-Khunsari, ma'abucin manyan talife talife a fannonin Musulunci masu yawa. Wannan ne ya share wa Imam fagen shiga fagen karatun addini don zama abin da ya zama a fannonin ilimi.
Tun yana karami ya fara karatuttukan share fage da suka shahara a cibiyoyin karatun addini na lokacin, wato Adabin Larabci (ilimin lakantar harshen larabci) da Mandiki (ilimin lakantar hanyoyin sahihin tunani) da Fikihu da Usulul-Fikih a hannun manyan malaman garinsu –Khumain. Ya fara karatunsa ne a hannun babban wansa Ayatullahi Sayyid Murtadha Basandideh al-Khumaini (saboda ya tashi maraya ne). Ban da shi kuma ya yi karatu a hannun malamai irin su Mirza Mahmud Iftikharul-Ulama, da Mirza Ridha al-Najafi al-Khumaini, da Sheikh Ali Muhammad al-Burjurdi, da Sheikh Muhammad al-Gholpegani, da Sheikh Abbas al-Araki. A shekara ta 1919 ne ya yi hijrarsa ta farko zuwa Arak don ci gaba da karatunsa a lokacin yana da shekaru goma sha bakawai da haihuwa. Bayan shekaru uku (a shekara ta 1922) ya tafi birnin Kum, inda saboda kaifin hazakarsa da kwazonsa ya share marhalolin kammala karatu da sauri irin na ban mamaki. A cibiyar ilimi ta Kum ya yi karatu a hannun manyan malamai irinsu Sheikh Mirza Muhammad Ali Adib, da Ayatullahi Sayyid Muhammad Taki al-Khunsari, da Ayatullahi Sayyid Ali al-Yathribi al-Kashani. Ya kuma yi karatun Furu'a mai zurfi a hannun shuganan Cibiyar Ilimi ta Kum na lokacin, wato Ayatullahi Abdul-Karim al-Ha'iri.
Imam bai takaita da ilmummukan da aka saba kwarewa a kansu a cibiyoyin ilimin addini na lokacinsa ba, kwadayinsa ga ilimi sun sa shi ya zurfafa karatun wasu darussa na gefe (a bisa tsarin lokacin) irin su Falsafa, wadda ya karanta ta a hannun Sayyid Abul-Hassan al-Rafi'i al-Kazwini. Haka ya karanta Irfani (Sufanci) a hannun Sheikh Mirza Ali Akbar al-Hakimi al-Yazdi. Ya karanta Aruli da Kafiyya (ilimin lakantar waken larabci) a wajen Sheikh Muhammad Ridha Masjid Shahi al-Isfahani; haka a wajen wannan malami ne dai Imam ya karanta Falsafar Musulunci da Falsafar Turawan Yamma. Sannan ya zurfafa ilimin da Irfani (Sufanci) na nazariyya a wajen Ayatullahi al-Haj Mirza Jawad al-Malaki al-Tabrizi. Bayan nan Imam ya share tsawon shekaru shida yana karantun Tarbiyya (Irfani na aikace) a hannun Ayatullahi Mirza Muhammad Ali Shah Abadi. Wannan malamin na karshe ya yi matukar tasiri a rayuwar Imam na tarbiyya, ta yadda ya rika yawan ambatonsa da yi masa addu'a a talife talifensa da zantukansa.
Cikin dan lokaci sai da Imam ya zama majingina a ilimi, saboda kwarewar da ya yi a fannonin Fikihu da Usulul-Fikh ta yadda sai da ya kai matakin ilimi na ijtihadi (ikon fitar da hukunce hukunce daga tushensu na asali) a lokacin samartakarsa, ban da kwarewa da ya yi a sauran fannonin ilimi da ambatonsu ya gabata. Wannan ya sa ya yi rata wa malaman zamaninsa, wadanda suka saba kwarewa a wani fanni (masamman na Fikihu da Usulul-Fikh) tare da sassauci a kan sauran bangarorin (masamman na Falsafa da ilumman hankali).
Wannan takaitaccen bayani kan rayuwar Imam ta dalibta ya nuna irin nisan da ya yi a gogayya da ilimi da malamai da yalwar iliminsa, wadanda su suka fi tasiri a ayyukan da ya gabatar daga baya na karantarwa da tarbiyya da jihadi da gwagwarmayar siyasa.

Malami Na Allah

Imam Khumaini (Kuddisa Sirruhu) ya bayar da kyakkyawan misalin nagartaccen malami. Yi masa kyakkyawar fahimta zai taimaka mana wajen riskar abin da ake ruwaitowa daga Manzo [SAWA] mai cewa: "Malamai magadan Annabawa ne." AlKur'ani kuwa ya bayyana ayyukan Annabawa da cewa shi ne "Tsarkakewa da Karantarwa." Imam ya aikata ilimi kwarai da gaske. Ya guji duniya da abin da ta kunsa na kyale-kyale, ta yadda har ya bar duniya a gidan haya yake zaune; bai mallaki gidan kansa ba (sai na gado da ya yi tarayya da 'yan'uwansa a kai). Haka bai damu da kyale kyale irin na sutura da motocin alfahari ba (bai ma taba mallakar motar kansa ba). Ya yi matukar tarbiyyar kansa ta yadda sai da masu kallonsa suka rika shaida siffofin kamala a tare da shi, masu sauraron zantukansa suka rika hakaito zubar hikima daga bakinsa, masu zama da shi suka wa'azantu daga dabi'unsa, har wasu sukan zubar da hawaye da ganinsa, saboda yadda yake tuna musu Allah Madaukaki.
Imam Khumaini ya yi aikin yada ilimi haikan, ta hanyar karantarwa da talife talife. A fannin karantarwa ya karantar da dalibai a fannonin ilimi a Makarantar Faidhiyya da Masallacin al-A'azam da Masallacin al-Muhammadiyya da Makarantar Al-Haj Mulla Sadik da Masallacin al-Silmasi duk a birnin Kum; ance daliban dake halartar karatuttukansa a wadannan wurare sun wuce dubu daya. Haka a lokacin zamansa a Najaf ta kasar Iraki ya karantar a Masallacin al-Ansari har na tsawon shekaru goma sha hudu (a nan ne ma ya fara bijiro da mas'alar Shika Shikan Gwamnatin Musulunci). Ta wannan hanya ce ya sami daman yaye wasu zakakurai wadanda suka kasance, kuma ba su gushe ba, masu misalta tunaninsa da halayyarsa, irin su Ayatullahi (Prof.) Shahid Murtdha Mutahhari (Allah Ya ji-kansa), da Ayatullahi Shahid Sayyid Baheshti (Allah Ya lullube shi da rahmarSa), da Ayatullahi (Dr.) Shahid Mufatteh (wanda ya hada baiwar zurfafawa a ilimin addini da na zamani). Sheikh Hashimi Rafsanjani da magajin Imam kuma ja-goran juyin Musulunci, Ayatullahi Sayyid Ali Khamina'i. Wadannan da ire irensu masu yawa sun haskaka da Imam a ilmance da tarbiyyance.
Bayan wafatin Ayatullahi al-Ha'iri ne wasu kwararru suka fara tuntubar Imam don rike akalar Marja'iyyar Kum (wanda shi ne matsayin addini da ya fi kowanne a tsarin Musuluncin Shi'a), amma tsantseninsa ya sa ya yi ta kau da kai. Sai ma ya shugabanci gungun wasu malaman Kum da suka nace har suka ga sun gamsar da Ayatullahi al-Burjurdi da ya baro Najaf ya dawo Kum don shugabatar Cibiyar.
Harkokin karatu da karantarwa ba su dauke hankalin Imam Kumaini daga talifi ba. A duk lokacin da ya fahimci bukatar wallafawa ko sharhi ko taliki a kan wani littafi yakan kebe lokaci don haka. Wannan ya sa Imam ya bar littafan da suka kai hamsin, tsakanin wadanda ya wallafa da wadanda ya yiwa taliki. Wasu daga cikinsu har yanzu ba a buga su ba. Daga wadanda aka buga an kididdige kimanin arba'in da biyar da suka hada da Kitabul-Bai'i (mai mujalladi biyar), da Bada'iul-Durar Fi Ka'idati Nafyil-Dharar, da Anwarul-Hidaya Fit Ta'alikti alal-Kifaya (kan Usulul-Fikh), da Sirrul-Salat, da Adaabul-Ma'anawiyyati Lis-Salat (duk a kan Irfani), da al-Hashiyatu ala Sharhi Fusus al-Hikam (wanda ya yi taliki a kan sharhin littafin Fusus al-Hikam na Ibin Arabi), da Misbahul-Hidaya, da al-Arba'una Haditha (inda ya zabi wasu hadisai arba'in ya yi sharhinsu kan kyautata hali da tarbiyya), da Jihadul-Akbar, da Manahijul-Wusuli Ila Ilmil-Usul, da Tahrirul-Wasila da wasu masu yawa.

Mujahidi Na Hakika

Karfin halin Jihadi saboda Allah da ruhin yunkurawa don tabbatar da adalci da kare mutuncin talakawa da wadanda ake zalunta da Imam Khumaini ke da shi sun samo asali ne daga akida da tarbiyyar gida da kyawawan dabi'u da zurfin ilimi da suka kewaye rayuwarsa, abin ya kuma hadu da tabarbarewar yanayin siyasa da na zamantakewa a duniya da Iran ta lokacin.
Imam bai fara yunkurin siyasa bisa tunanin kau da gwamnatin ba; ya fara ne da nasiha ga mahukunta da tsawatar da su a kan zalunci da irin makauniyar biyayyar da suke yi wa 'yan mulkin-mallakan kasashen Gabashi da Yammaci. Wannan ya sa ya rika bibiyar kudurorin hukuma da yadda take gudanar da mulki sau da kafa don cimma haka. Misali a ranar 8/10/1963 a gab da zabubbukan majalisun kananan hukumomi, gwamnatin Iran ta lokacin ta fitar da dokar share sharadin Musulunci a kan masu zabe da 'yan takara; haka nan ta musanya rantsar da zababbun wakilai da AlKur'ani zuwa rantsar da su da kundin tsarin mulki. Imam ya yi matukar adawa da wannan mataki, kuma ya sa shi ya zama asasin fadakar da jama'a wajen bijere wa gwanmatin Shah Ridha Pahlawi.
Imam bai kyamaci akidar "a shiga a gyara ba"; abin da ya kyamata shi ne "a shiga a zagwanye", wato tasirantuwa da mummunan yanayi. Wannan yasa ya yi amfani da hanyoyin gyara ta ciki da wajen hukuma; domin kuwa ya tura muridansa cikin gwamnati don kara kyautata abin da bai baci ba, da gyara mummunan yanayin da ya baci gwargwadon iko. Kamar yadda ya yi amfani da wadanda ba sa cikin gwamnati wajen ganin kiransa na kawo gyara ya yi tasiri, wannan ne ma ya sa juyin da ya ja-goranta daga baya ya hado kowa da kowa.
Imam ya iya hado kan da yawa daga malamai da daliban addini da na jami'o'i wajen shiga sahun hamayya da matakan gwamnati da suka zama hadari ga addini da al'umma a wannan kasa da musulmi suka wuce kashi casa'in da takwas bisa dari na duk al'ummarta. Wannan ya kuwa faru ne saboda yadda suka san cewa a tsawon rayuwarsa ya kasance tare da su (ta hanyar kasancewa dalibi ga wasu kuma malami ga wasu); ga shi dan kasa na gari da 'yan boko suka san shi da kishin kasa da taimakon jama'a. Tare da duk wadannan, ga yadda ya iya bayyana manufofinsa da kare su daidai da ka'idojin Musulunci ta yadda kowa ya fahimta. Kamar haka ya sami amincewar talakawa saboda kyawawan dabi'unsa da taimakonsa gare su da kulawa da rayuwarsu da lafiyarsu da son ci-gabansu da suka sani daga gare shi tuntuni.
Sabanin yadda Turawan Yamma ke son nuna shi, Imam ya kasance mai tausasawa a kiransa. Bai tsananta wa sarki Shah da mukarrabansa ba, duk kuwa da halin taurin kai da rashin jin nasiha da girman-kai da suka rika nunawa.

Shugaba Na Kowa Da Kowa

Bayan kafa gwamnatin Musulunci Imam ya misalta adalcin nan na Musulunci a kan al'umma. Ya kare mutuncin wadanda ake zalunta a kasashen duniya ta hanyar taimakon gwamnati da kariyar siyasa da addu'o'i. Bai taba gafala daga abin da ya shafi al'ummar Musulmi a duniya ba. Ya sauke nauyin da ya hau kan malaman addini kan hadin kai da al'amarin Falasdinu da mafi kyawun fuska. Ya samar wa al'umma da alkibla a lokacin da ake neman ruda ta da tsare tsare na yaudara a fannonin rayuwa. Ya daukaka matsayin al'ummar Musulmi a duniya ta hanyar kare mutuncinta da 'yancinta. Ya sadaukar da jin dadin mutanen kasarsa don kare martabar wadanda ake zalunta a duniya. Sai ga taimakonsa da goyon-bayansa sun isa ga 'yan gwagwarmayar neman 'yanci a Afrika Ta Kudu da Nicaragua da Namibiya. Ya bude kofofin Jumhuriyar Musulunci ga 'yan gudun hijra makota daga Afganistan da yaki ya daidaita, da wadanda suka gudo daga Iraki da mulkin danniya da kama-karyar Saddam Hussain ya hana numfashi, da sauran kasashen da aka hana 'yancin addini a tsohuwar Tarayyar Sobiet. Ya daidaita tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba a wajen adalci da 'yanci. Ya kawar da kai daga bambance bambancen mazhabobin musulmi, yayin da ya hada hankalinsa a kan abubuwan da suka hada kan Musulmi. Ya fitar da mata daga kangin bautar jiki da biyan bukatun maza zuwa bautar Allah da karimci. Mace ta yi kafada-da-kafada da namiji a fagagen rayuwa da ciyar da al'umma gaba bisa karantarwarsa.
A karshe ina cewa ne Imam samfuri ne na dalibi mai kokari da naci da aiki da ilimi, kuma misali ne mai kyau na nagartaccen malamin addini da bai taba kawar da kai daga ainihin ayyukansa na karantarwa da tarbiyya ba, mai kishin kasarsa da mutanensa da addininsa da bai taba sayar da daya daga wadannan ko watsar da shi da ci-gabayansa ba, miji na gari mai tausayi ga iyalinsa, uba mai tarbiyya da kulawa ga 'ya'yansa, gwarzon namiji da bai san tsoro ko ja da baya ba, shugaba mai adalci da bai bambanta kansa da talakawa da masu karamin karfi ba.
Wannan taliki zai saura abin koyin 'yantattu da wadanda suka fahimci manufar samuwarsu a duniya. Allah Ya saka masa da alheri a kan abin da ya gabatar ga 'yan Adam.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
9+1 =