Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

RAYUWAR AYATUL-LAHI UZMA SAYYID MUHAMMAD RIDHA MUSAWI GULPAIGANI (K)Malamai su ne masu gadon ilimin annabawa kuma wakilai ne na Imam zaman Imam Mahadi (a.s) wurin yada koyarwar Ahlul Baiti (a.s).
Malamai su ne katanga mai karfi ta kariya ga gidan tauhidi da sakon manzanci da wilaya, kuma su ne taurari masu walkiya a sama.
Ayatul-Lahi sayyid Muhammad Ridha musawi Gulpaigani malami ne da ya rayu a cikin rabin karnin da ya gabata, jagora kuma mar’ja’in Shi’a wanda ya kasance mabubbugar alherin Allah na al’adun mutane da zamantakewarsu da ya assasa al’amuran kamar haka:

1. Shekaru tamanin yana koyon karatu yana koyarwa
2. Shekaru 40 yana jagorantar hauzar ilimin shi’a
3. Assasa makarantar Ayatul-Lahi Uzma sayyid Muhammad Ridha musawi Gulpaigani
Akwai kuma karatuttukan cikin Sidi da Laburaren littattafai da suka hada da:
4. Assasa Mu’assasar Darul Kur’ani, da koyar da Kur’ani ga dubunnan dalibai a duk fadin Iran da kuma yada Kur’ani da sunan hauzar Kum da aika shi duk duniya da hada tafsirai da yarurruka daban-daban na farisanci da larabaci.
5. Kafa cibiyar nan ta Mu’ujamul Fikihi da sabon ci gaban nan na Komputa domin yada ilimi da koyarwar Ahlul Baiti (a.s)
An samu natija mai albarka sakamakon haka da ta hada da:
a. Samar da Sidin Mu’ujam na fikihu da hadisi da Usul da sauran ilimomi da suka kai dubunnai.
b. Sidin Imam Mahadi (a.s) da ya hada da Kur’ani da Nahajul balaga, da Sahifar Sajjadiyya, da Mu’ujamu ahadisul Mahadi.
c. Kamus din Fikihu
d. Tsarin bayanin tarihin malamai a zamuna daban-daban
e. Tsarin Babobin fikihu na dukkan littattafan shi’a da karatunsu
f. Tsarin Sanin sunayen littattafai da kuma sanin littattafan da marubuta suke bukata da adres dinsu da yiwuwar bincikensu
6. Hidimar al’umma da mutane
a. Samar da asibiti domin saukake magani ga dalibai da sauran mutane wadanda suka samu rashin lafiya sakamakon yaki da dagutu, da kuma yakin kariyar kai da aka yi kan harin kasar Iraki
b. Gina Madinatuz Zahara ta Labanon
c. Fadada masallacin Imam Hasan Askari da yake birnin Kum, da fadin murabba’in mita dubu ishirin da biyar
d. Kafa wani asibitin mai gadon marasa lafiya na kwanciya har guda dari mai fadin murabba’in mita dubu bakwai
e. Assasa da gina gomomin gidajen malamai a Kauyuka da na makarantar Kur’ani
f. Assasa gomomin masallatai da makarantun addini a kauyuka da na makarantar Kur’ani
7. Hidimominsa na duk fadin Duniya
a. Assasa majma’ul islami a London wanda yake daya daga cibiyoyin Shi’a a kasashen Turai da ya samar da albarkar wayar da mutane da yada ilimi a Ingila da sauran kasashen Turai, hada da cewa akwai mutan masu yawa da suka fahimci mazhabin Ahlul Baiti (a.s) ta wannan cibiya gashi kuma har ila yau kuma mafi girman sallar juma’ar Shi’a da ake yi a London a wannan cibiyar ne ake yin ta
b. Assasa makarantar Amirul Muminin a (Kuwaiteh da take a Pakistan)
c. Assasa Makarantar Ayatul-Lahi Hakim a Rawalfandi a Pakistan
d. Madinatuz Zahara a Labanon
e. Darul aitam a Labanon
8. Yin ayyukan jagoran juyin musulunci a ayyukan hajji
• Raba dubunnan littattafai da suke kariya ga mazhabin Ahlul Baiti (a.s) a tsakanin alhazawan duniya daga kasashe daban-daban
• Amsa tambayoyin hukunce-hukuncen shari’a da na akida ta hannun malamai
Hidima da shiryar da alhazawa ta hanyar yada littattafan ladubban hajji da ayyukansa da mas’alolin shari’a
9. Rubuce-rubucensa
• Ta’alikin littafin Urwatul wuska
• Ta’alikin littafin Durrul fawa’id na sheikh Abdulkarim Ha’iri
• Littattafansa: Littafin Hajji, Littafin Kadha, Littafin Sheda, Littafin Haddodi, Littafin Hukunce-hukuncen mata, Littafin sallar jumma’a, Littafin al’hidaya game da mas’alolin hukunce-hukuncen addini, da kuma Risaloli goma a kan babobi daban-daban na Fikihu.
10. Dabi’arsa da halayensa
• Ibada: Ya samu dacen halartar haramin ma’asuma na kusan shekaru 70
• Kur’ani: yana karanta Juzu’I biyu ko daya na kur’ani a kullum, kuma yana samun wani hali na musamman yayin karantawa, yana cewa: Mafi girman wa’azi shi ne Kur’ani idan an karanta shi da tadabburi da lura da la’akari da kuma kauna da mika soyayya ga Ahlul Baiti tsarkaka (a.s).
• Yana tafiya da kafafuwansa har zuwa Kabarin ma’asuma tare da masu kukan juyayin sayyida Zahara (a.s)
• Yana yin zaman makokin sayyidus Shuhada Imam husain (a.s) a gidansa a kowane sati, kuma duba zuwa ga marja’ancinsa da iliminsa yana cewa: Ina fatan a tabbatar da sunana cikin masu karanta juyayin Sayyidus Shuhada (a.s)
• Cikakken ladabi: Kaskan da kai, da hakuri, da tsari, suna daga cikin tabbatattun dabi’unsa na gari
11. Al’amuran Siyasa: Sayyid Ayatul-Lahi Ali Khamna’i yana cewa: Ayatul-Lahi Uzma sayyid Muhammad Ridha musawi Gulpaigani yana daga cikin ginshikan amodan juyin musulunci da tsarin hukumar musulunci, kuma a lokacin da Imam khomain (k) ya kasance an kore shi kasar waje muryarsa ce kawai sautin marja’iyya da ya rage wanda yake tashi daga yana mai karfafawa da yin kaimi ga gwagwarmayar juyin musulunci a cikin halaye da yanayoyi masu wahala matuka da gaske
12. Idan mun duba abin da ya fada game da wafatin Imam Khomain (k) yana cewa:
Mutum ne wanda ya amsa wa kiran Allah da gaskiya, wanda da kokarinsa da sadaukarwarsa ne ya jagoranci duniya da gaskiya a wannan zamani namu, kuma ya isar da takbiri da kiran tauhidi da kadaita Allah zuwa ga kunnuwan mutanen duniya, kuma da wannan ne girma da daukakar musulmi ta dawo, kuma kiransu ya kai zuwa ga kunnunwa masu girman kai na duniya masu da’awar karfi ya girgiza su.
Ya fada a cikin wasiyyarsa a doka ta uku cewa: Kiyaye asalin samuwar jamhuriyyar musulunci dole ne, kuma kada masu iko a hannu su sake su karkace daga wannan tafarkin, kuma su yi kokarin ganin sun kare wannan tsarin da kokarin ya yi daidai da na musulunci a kullum.
Haka nan ya karfafa samuwar zamar hauza da kanta ba tare da dogara da daula ba.
Kuma Ayatul-Lahi Makarim Shirazi yana fada cewa ya ce: Ina karfafa wa dalibai cewa dole ne su fi karfafa kyawawan halaye a gefen iliminsu, kuma hauza ta kasance tana zaman kanta ne har abada.
Bayan mutuwarsa ce mabiyan mazhabar ahlul bait (a.s) suka yi juyi a duk fadin duniya.
Shi hakika yana daga cikin malaman da suka siffantu da wannan hadisi madaukaki da yake cewa; “mai kariya ga kansa, mai kiyaye addininsa, mai saba wa son ransa, mai biyayya ga umarnin jagoransa”. Kuma ya rasu a daren jumma’a 24 ga Jimad Sani 1414, da ya yi daidai da 18 ga Azar 1372, yana da shekaru cas’in da takwas.
Allah ya ji kansa ya gafarta masa.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+10 =