Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

ASSAHIB BN UBBAD, BABBN MUTUM MAI KIMA


Na Sa’ib Abdulhamid


Ana ganin Sahab dan Ubbad daya daga cikin wazirai a daulolin musulunci. Kuma daga mafificinsu azama da kwazo, kuma daga wadanda suka yi fice a adabi da ilimi da wallafawa, kuma ya hada falaloli masu yawan gasket fiye da wazirai da kuma mafi yawan sarakuna ma.
Ba abin mamaki ba ne idan ka samu bayanai sama da dari da hamsin game da shi gun ma'abota adabi:
Shi dai shi ne Abul kasim, Isma'il dan Ubbad dan Abbas dan Ubbad, dan Ahmad dan Idris, addilami al'ispahani, alkazwini, attalikani. An haife shi a zul'ka'da 326, H. ko 324 H. a garin Isdahar na Farisa, kuma ya rasu Rayyi an kai shi Ispahan a shekarar 385 H.
Shi masani ne mai girma kuma malamin adabi, kuma waziri mai taimako, wanda ake yi wa lakabi da wanda ya isar wa wadanda suka isar.
Kuma an yi magana game da yabonsa mai yawa matuka, kuma dukkan yabon da aka yi masa yana cikin wadannan kalmiomin guda biyu:
Na farko: Abu mansur sa'alabi yana cewa: Ba ni da wata kalma da zata zo da zan iya yabonsa da ita game da iliminsa da adabinsa, da girman sha'aninsa a baiwa, da kuma kebantarsa da kyawawan kalmomi.
Na biyu: fadin nan na Yakutul hamawi: …Ya kasance yana da falala da ba abin da za a ce sai yabo da bayanin baiwarsa, kuma zarginsa ya kasance yabo ne gareshi.
Ya kasance ana yi wa mahaifinsa lakabi da amintacce, kuma ya kasance ya zauna da Ibnul amid da wazirin Ruknuddaula, don haka ma aka kira shi da Sahib.
Ya kasance mutun ne mai saurin fushi, mai kwarjini, sai dai duk da haka yana da dadin zama yana cewa da abokan zama: Mu da rana sarakuna ne, da daddare kuwa 'yan'uwa ne. ya kasance mai kaifin harshe, mai saurin ganewa, mai amsawa da wuri.
Hilal dan almuhsin yana cewa: Bai taba ganin mutane sun yi bakin ciki ba irin na rasuwar sahib, yayin da aka sanya shi cikin akwati za a kai shi makabarta sai mutane suka riki kasa a hannyensu suka tsaya gaba daya a gabansa, suka kona tufafinsu suka mari fusakunsu, suka kai matuka wurin yin kuka da ihu.
Ya kasance mutum ne mai balaga da fasaha, matuka, kuma masu tarihinsa sun yi sabani kan cewa shi ba'mu'utazili ne ko Shi'a, sai dai an fi karfi kan cewa shi Shi'a ne, saboda dalilan da ake kawowa kan mu'utazilancinsa duk masu rauni ne.
An nakalto maganganu masu yawa game da maganganunsa game da tabbatar da imamancin Imam Ali (a.s), sannan kuma ya wallafa littattafai masu yawa.
Ya kasance duk da yana da asali daga farisanci amma yana fifita larabawa a kan waninsu, ya kasance yana cewa duk wanda yake fifita farisawa kan larabawa to ina ganin yana da jinin majusanci. Ya kasance a rayuwarsa yana da masu suka da masu yabo da yawa game da tarihin rayuwarsa.
A game da tsantseninsa ana cewa wata rana ya ce a kawo masa abin shansa sai aka kawo masa, yayin da aka zo da shi sai wasu suka ce kada ka sha akwai guba! Sai ya ce meye dalilin hakan? Sai aka ce: ka ba wa mai hidimar da ya kawo ya sha. Sai ya ce: ba zan yi haka ba, kuma ban yarda ba. Sai aka ce ka jarraba a kan kaza. Sai ya ce: ba zan kashe dabba mai rai ba. Sai ya ce; a zubar da shi, sannan sai ya ce da mai hidimar kada ka sake shiga gidana har abada, amma ya yi umarni duk wata a rika ba shi albashinsa, ya ce: Ba zamu ture yakini da kokwanto ba!
Haka nan sahib ya kasance yana da wani aboki da ake ce masa makki ya kasance yana munana masa sai ya yi umarni a daure shi, sai wata rana ya hau saman rufi yana kewaya sai ya hango abokinsa a dakin da ya ce a rufe shi, sai abokin nasa ya ce: "sai ya duba sai ya hango shi a cikin wutar jahima" sai ya sahib ya ce: "Ku yi shiru a cikinta kada ku yi mini magana". Sannan sai ya yi umarni a sake shi.
Sahib ya rubuta littattafai masu yawa kan ilimomi daban-daban kamar sanin Allah da tarihi, da akidu da likitanci, da ilmomi daban-daban, da lugga da adab, da hikimomi, da wakoki.
Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
9+9 =