Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Ku yi mana bayanin yadda motsin kawar da zaluncin Duniya na imam Mahadi (a.s) zai fara? yaya zai fara? kuma ta ina ne zai fara?


Kowa yana son ya san mene ne zai faru a zamanin da Imam Muhammad Mahadi (a.s) zai zo? kuma daga ina ne zai fara motsawa? kuma da wane mutane ne zai samu gwabzawa? kuma yaya zai yi galaba kan dukkan Duniya har ya samu kama Duniya gaba daya? wadannan tambayoyi ne da suka cika kwakwalen masu bege da sauraro, da masu tambayoyi masu yawa. Amma fadin abin da zai faru nan gaba wani abu ne mai wahala da ba zai yiwu ba ga kowane mutum, sai dai muna iya kawo wasu abubuwan da suka zo a dunkule a ruwayoyi.

A zamanin da duhun zalunci ya cika Duniya, azzalumai suna rashin mutunci da danniya, su kuma sauran al'umma suna neman mai ceto wanda zai kama hannunsu; sai ga kira daga sama a cikin daren wata Ramadan yana albishir da zuwan wanda aka yi alkawarin zuwansa [1], a lokacin ne zuciya mai kaguwa zata saurari wayewar wannan gari. A wannan zamani kuwa Sufyani ya kama yanki mai fadi na Siriya da Jodan da Palasdin, kuma ga rundunarsa tana kan hanyar Makka domin neman Imam Mahadi (a.s), da za a kisfe su a wani wuri mai suna Baida'u. [2]
Bayan shahadar Nafsu zakiyya da wani dan lokaci sai Imam Mahadi (a.s) ya bayyana wani saurayi a masallacin Makka mai alfarma, a lokcin rigar Manzon Allah (s.a.w) mai albarka tana jikinsa, kuma yana jingina da dakin ka'aba tsaknin rukuni da makam Ibrahim (a.s), bayan godiya ga Allah da kuma salati ga Manzon rahama (s.a.w) da alayensa sai ya ce: Ya ku mutane mu muna neman taimakon Allah ne, kuma duk wanda ya amsa kiranmu, muna neman taimakawarsa.
A lokacin sai ya sanar da kansa ga mutane kuma ya sanar da iyayensa: ku ji tsoron Allah kan hakkokinmu kada ku ki taimaka mana, ku taimaka mana Allah madaukaki zai taimake ku. Daga nan ne fa sai mutanen sama su riga na kasa amsa masa kiransa, sannan sai jama'a jama'a su gangaro domin yi masa bai'a, a lokacin da Jibril (a.s) ya kasance mai rakiya ga Imam Mahadi (a.s), sai ga mutane 313 daga sahabbansa na musamman su ma sun zo su yi masa bai'a, bayansu kuma sai wasu mutane rundunar mayaka dubu goma su zo tantinsa domin su yi wa dan Manzon Allah bai'a. [3]
Sai kuma Imam Mahadi (a.s) ya daga tutar yaki ya salladu da gaggawa a kan Makka da gewayenta, sannan ya kawar da miyagun bayi da masu barna daga wadannan yankuna, sannan sai ya kama hanyar Madina domin samar da adalci da tausayawa ga bayi. Daga nan ne kuma sai ya tafi Iraki birinin Kufa domin ya rike shi cibiyarsa kuma hedkwatarsa wacce daga nan ne zai tafiyar da al'amuran Duniya, kuma ya kira dukkan mutanen Duniya zuwa ga hukunci da Kur'ani da dokokin Allah madaukaki.
Imam Mahadi Jagoran Duniya shi ne mabudin asasi na cimma nasara, domin yana da taimakon Allah na musamman bayan muminai mataimaka da yake da su, kamar dai lokacin Manzon Allah (s.a.w) da aka taimaka masa da tsorata makiya kafin ya yake su, don haka Allah yana da ikon sanya firgici a zukatan makiya, ta yadda ba su da wani iko na yin taho mu gama da Imam Mahadi (a.s).
Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: Imam Mahadi (a.s) zai samu taimako daga firgici da tsoro. [4]
Cin nasara da kama baitul mukaddas wani abu ne mai ban sha'awa [5], wannan al'amari mai albarka zai faru ne a lokacin da Annabi Isa (a.s) zai sauko daga sama, kamar yadda muka sani shi rayayye ne kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma, kuma zai karfafi gwagwarmayar Imam Mahadi (a.s), sannan kuma zai yi masa bai'a ya yi salla a bayansa, wannan kuwa tana nuni uwa ga fifkon Imami na goma sha biyu (a.s) ne kan Annabi Isa (a.s).
Manzon tsira da aminci yana cewa: Na rantse da wanda raina yake hannunsa, da rayuwar Duniya ta kasance saura wuni daya rak, da Ubangiji ya tsawaita wannan rana har sai dana Mahadi (a.s) ya tashi, sannan sai Isa dan Maryam (a.s) ya zo ya yi salla a bayansa. [6]
Da wannan ne jama'a mai yawa daga Kiristoci zasu yi bai'a ga ajiyar Allah kuma jagoran Shi'a masoya iyalan gidan Annabi (s.a.w) Imam Mahadi (a.s), kai kana iya cewa; Annabi Isa (a.s) ya ajiye wannan rana ne domin ya nuna wa mutanen Duniya gaba daya hanyar shiriyarsu. Koda yake bayyanar mu'ujizozi a hannun Imami Jagora (a.s) yana daga cikin tsarin da ya yi domin kawo shiriya ga Duniya baki dayanta.
Don haka ne ma Jagora (a.s) zai tono allunan Attaura da ba a canja su ba -wato littafin Yahudawa mai tsarki- wadanda aka binne su a wani wuri a wannan Duniya [7], kuma Yahudawa su ga alamomin jagorancinsa a wadannnan alluna, sannan sai su yi imani da shi. Haka nan mabiyan sauran addinai zasu ga irin wannan canji mai girma, kuma da ganin wannan kira na Imami mai gaskiya da kuma mu'ujizozisa, sai su zo jama'a jama'a suna masu yi masa bai'a, kuma alkawarin Allah madaukaki ya tabbata, musulunci ya daukaka a ko'ina a Duniya.
"Shi ne wanda ya aiko Manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin ya yi galaba a kan addini dukkaninsa, kuma koda kuwa mushirikai sun ki". [8]
Idan an yi la'akari da abin da aka fada a nan zamu ga cewa babu wani wanda zai rage bai mika wuya ba sai azzalumai wadanda suke shirye su tsaya gaba da gaba da gaskiya, wadannan kuwa ba su da karfin tsayawa domin yakar muminai, kuma zasu samu sakamakon aikinsu da takobin adalci ta Imam Mahadi (a.s), kuma Duniya da mutanenta zasu kubuta daga sharrinsu na har abada.


1. Gaiba, Nu'umani, babi 14, h 17.
2. Biharul anwar, j 53, shafi: 10.
3. Gaiba, Nu'umani, babi 14, h 67.
4. Kamaluddin, j 1, babi 32, h 16, shafi: 603.
5. Ruzgare rahayi, j 1, shafi: 554.
6. Biharul anwar, j 51, shafi: 71.
7. Ruzegare rahayi, j 1, shafi: 522.
8. Tauba: 33.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+5 =