Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


AHMAD KUWASI HANIF
(Kanada - Kirista)An haife shi a shekarar 1956 a Tsuburin nan na Tirinidada wanda yake a Kogin Karibiyan. Kuam wannan wuri ne da aka san shi da hatsari da hatsabibanci da kuma rikicin siyasa saboda dalilai masu yawa.

Kuma mutanen wannan yankunan domin su samu zaman lafiya sai su yi hijira imma dai ko Amerika ko kuma Kanada, sai ya yi hijira zuwa Kanada ya shagaltu da cigaban karatunsa har ya samu digiri na xaya a siyasa da kuma wani a kan ilimin rayi.

Farko

Sannane cewa baqaqe a waxannan yankunan amerika suan fama da wahalhalun wulaqanci kamar yadda kowa ya sani sun zo ne bayi a lokacin mulkin ‘yan mamaya na Potugal da Biritaniya da Faransa kuma ‘yan kasuwa ne suke kawo su , don haka sai suke fuskantar abin da mazauna wurin na jajayen indiyawa suke fuskanta na dukkan muzantawa hatta da na al’ada bayan na tattalin arziki. Amma duk da haka lokaci yana tafiya sai ga baqaqe sun kasance jama’a mai yawa sosai.

Musulunci kawai

Don haka sai ya shiga neman abin da yake mafita gareshi kamar dai yadda sauran baqaqe suke yi na neman ko kwaminisanci ko wani abu daban, har dai ya kai ga cewa ba shi da wata mafita sai musulunci kawai.

Yana cewa dalilin da ya sanya baqaqe rungumar musulunci saboda musulunci shi ne addinin da ya fi kowanne yaxuwa a kasashen Amurka, wannan kuwa yana komawa ne ga cewa a musulunci babu wani batun wasu xabaqoqi na wasu mutane daban, shi na kowa ne musamman raunanan mutane ababan zalunta, kuma ga baqaqe sun rasa al’adunsu kuma kiristanci yana ba su al’adun riqo da duniya ne, amma musulunci yana xamfara su da Ubangiji ne.

Wani dalilin da ya sanya baqaqe karvar musulunci shi ne baqanta shi da jaridu suke yi kullum, sai dai baqaqe ba sa karanta jaridu domin suna ganin ta a matsayin kayan yammacin duniya ne da yake zaluntar su. Kuma su suna qin duk abin da ya shafi daula ne.
Amma wani abin takaici shi en yadda wasu suka bar shi saboda ya musulunta a duniyar yamma da ake kiran ‘yancin komai musamman na tunani da aqida.

Samun canji

Saboda ya samu qarfafuwa da shiriya sai ya daxa bincikensa kan musulunci, a nan ne ya samu gaskiyar da take ta haqiqar musulunci da ta sanya shi inganta imaninsa , kuma wannan ya kai shi ga riqo da mazhabin ahlul bait (A.S), yana cewa: sai na samu cewa wannan mazhabin yana sama da dukkan wani tunani na zamani a duniyar siyasa, kamar yadda shi ne kawai mazhabin da yake iya kare kansa saboda yadda yake qunshe da asasin musulunci mai qarfi, kamar yadda shi kaxai ne yake iya tabbatar da gina al’ummar wannan zamanin, a taqaice dai:

Wannan mazhabin ya samu tabbatar da cin nasara a wannan duniya a qarni na ishirin.
Kuma ya qara da cewa: abu na biyu shi ne yadda ya samu tasirantuwa da wasu littattafai kamar haka:
1. Tarihin shida daga Imam Ali (A.S) zuwa Imam Sadiq (A.S).
2. Shi'a na allama Tibatiba’i
3. Asalin Shi'a na Kashiful Gixa’
4. Al’irshad na Sheikh Mufid.
5. Almuraji’at na sayyid sharafuddin.
Sai ya samu cewa a musulunci akwai vangarori biyu:

Na farko: Vangaren Ahlul bait (A.S) da jama’arsu kuam su ne suke qin yaqi da xauki ba daxi da zalunci da danniya.
Na biyu: Vangaren masu mulki da masu bin su kuma suna ganin bai halatta ba kawar da ita.
Sai al’adun nan na shahada a musulunci na Ashura da yake cikin mazhabin ahlul bait (A.S) shi ne ya fi qarfi wanda da shi ne musulunci yake xaukaka a duniya.

Ayyukansa

Yana yin tabligi a Kanada wani lokaci a tsakanin musulmi baqaqe.
Yana yin laccoci a jami’o’I da kuma cibiyoyin ilimi.
Yana karatun Hauzar ilimi a fiqihu da aqida da tarihi.
Yana da maqaloli game da al’amura daban-daban bai kevanta da musulunci ba kawai.

Gudummuwarsa ta shiryarwa

Ya samu dammar shiryar da mutane huxu (maza biyu mata biyu) kuma haxa da fahimtar da xan’uwansa ya yi tare da shi a wannan lokacin a shekarar 1982 a Jami’ar York a garin Toranto a Kanada.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+5 =