Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Me Ya Sa Allah Ya Halicci Shedan?


Na farko yana da kyau mu gane cewa; shedan suna ne day a shafi dukkan wani mai halakarwa da karkatarwa da batarwa daga tafarkin gaskiya da shiriya zuwa tafarkin karya da bata, kuma yana iya kasancewa mutum ko aljani. Amma Iblis suna ne na daya daga cikin mala’iku ko aljanu bisa sabani, wanda ya ki yi wa annabi Adam as sujada, kuma ya dauki alkawarin halakar da ‘ya’yansa gaba daya in banda masu ikhlasi daga cikinsu da Allah ya dauki alkawarin kare su daga kaidinsa da makircinsa.
Don haka tun farko Allah bai halicci Iblis don ya zama shedani da yake batar da mutane ba, ya halicce shi ne domin ya bauta masa, ya kuma taimakawa sauran bayi da yin ayyukan alheri da zasu samu tsira da rabauta da yin su, kuma ya kasance daga masu bautar Allah (s.w.t) daga cikin mala’iku, kuma kada mu manta cewa an halicce a matsayin halitta mai zabin kansa babu tilasta masa a kan ayyukansa.
Kuma duk da ya kasance daga cikin masu bautar Allah na koli, kuma yana daga cikin masu bauta da rusuna wa ubangiji madaukaki, sai dai yayin da aka umarce shi da yin sujada ga annabi Adam as sai ya ki, ya yi taurin kai. Don haka sai ya fado daga waccan daraja da ya samu, ya kasance cikin wadanda Allah (s.w.t) ya kore daga rahamarsa, don haka ne ma ya yi alkawarin yin waswasi a zukatan mutane domin halakar da su, da batar da su daga tafarkin shiriya. Sai dai babu wanda zai halaka da waswasinsa sai mai son rai, wanda ya biye masa. Duba ayoyin nan na surar Sad (S): 71-85.
Sai dai wani yana iya cewa; To tun da Allah ya san zai halakar da bayi don me ya halicce shi, domin Allah (s.w.t) ya san abin da zai faru tun kafin ya faru?
Amma idan muka duba amsar da muka bayar a farko tana iya gamsar da mu, domin wanda ya yi wannan tambayar muna iya tambayarsa cewa; shin Allah (s.w.t) ya san cewa mafi yawancin bayinsa zasu saba masa kuma ya halicce su ko kuwa? Kamar dai maciji ne da zai tambayi Allah madaukaki cewa; Ya ubangiji don me ka yi mutum alhalin ka san zai cutar da ni? a lokaci guda kuma shi ma mutum yana tambayar cewa; ya Allah don me ka yi maciji alhalin ka san cewa zai cutar da ni?
Don haka wannan bahasin yana koma wa zuwa ga bahasin cewa; shin akwai sharri cikin halitta ko kuwa babu sharri dukkaninsu alheri ne. Muna iya cewa babu sharri a cikin halittun Allah dukkaninsu alheri ne, sai dai sharri yana zuwa ne daga kiyasta wani wata tawaya idan an danganta ta da yadda ya kamata abu ya kasance.
Muna iya cewa a misali; kaifin wuka, da ita kanta wukar dukkaninsu alheri ne, domin halitta ce, haka nan taushin jiki da kasancewarsa mai karbar yankuwa alheri ne domin dukkaninsu samuwa ne. Amma sharri yana iya kasancewa ne idan wuka ta yanka jiki saboda kiyasta cewa; jikin bai kamata ba jinni ya fita daga cikinsa, ba domin kasancewar fitar jinni ita kanta sharri b ace, domin karbar yankuwa din kamala ne ga jikin ba sharri ba ne.
Misalin ciyawa ce a gona da take alheri ce, domin shuka ce, kuma halitta ce ta Allah (s.w.t), amma tana iya kasancewa sharri ce idan ta takura wa masarar da aka shuka, ko dawa da gero da ake nomawa. Don haka ke nan sharri ba shi da samuwa, ana iya fahimtar sharri ne idan an kiyasta yadda ya kamata abu ya kasance da yadda ya kasance.
Don haka Iblis shi kansa ba sharri ne ba ne, alheri ne, sai dai yana iya zama sharri ne idan an kiyasta cewa bai kamata ya kasance haka ba, domin ya kamata ya kasance bawan Allah ne da yake waswasin alheri ga mutane, saboda wannan ikon da Allah ya halitta masa na yin waswasin alheri, ko yin wasawasin sharri a zukatan halittu.
Kamar dai wuka ce, da ciyawa da suke alheri ne, amma ana danganta musu sharri domin kawai suna da wata rawa da zasu taka wurin wani tasiri da yake mayar da wani abu ba yadda ya kamata ya kasance ba.
Sannan wannan tambayar ta cewa; don me ya sa aka halicci Iblis tana iya hawa kan kowane halitta mai saba wa Allah da halakar da mutane da batar da su, domin wannan lamarin na halakarwa da batarwa bai kebanta da Iblis ba.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
5+8 =